Shugaban NDC a Kano Ya Fara Tutsu, Ya Zargi Kwankwaso da Ƙoƙarin Ƙwace Masu Jam'iyya
- Shugaban NDC a Kano, Usaini Isa Mai Riga ya ce ba zai miƙa tsarin jam’iyya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
- Ya bayyana cewa ba a cimma matsaya game da yadda za a tafiyar da NDC ba, kuma ba zai lamunci takun Kwankwaso da mutanensa ba
- Ya zargi Kwankwaso da shigowa tana nuna masu Izza, sannan ya ki sauraron mutanen da ya tarar suna tafiyar da NDC tun da farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sabon rikici na siyasa ya ɓarke a cikin NDC a Kano, yayin da shugaban jam’iyyar na jihar, Usaini Isa Mai Riga, ya bayyana ƙin amincewarsa da miƙa ragamarga tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Hon Mai Riga ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da aka yi na cimma matsaya da Kwankwaso kafin shigowarsa cikin jam’iyyar bai yi nasara ba, duk da an gudanar da taruka biyu daban-daban domin tattauna tsarin shugabanci.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da Premier Radio da aka wallafa a shafin Facebook na kafar, Mai Riga ya ce an fara samun matsala da Kwankwaso saboda izza.
Kwankwaso: NDC ta samu matsala a Kano
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa shugaban NDC na Kano, Hon Usaini Isa Mai Riga Kwankwaso ya shigo da zummar karɓe ragamar jam'iyyarsu baki daya.
Ya ce:
“Yana son mu miƙa masa gaba ɗaya jam’iyyar, duk da irin sadaukarwa da lokacin da muka bayar wajen gina ta lokacin da babu mai kula da ita.”
Mai Riga ya jaddada cewa wannan buƙata ba za a amince da ita ba, yana mai cewa shugabannin da ke kan mulki a yanzu za su yi tsayin daka wajen hana duk wani yunƙuri na ƙwace ikon jam’iyyar daga hannunsu.
NDC za ta kare hakkinta – Mai Riga
Usaini Isa Mai Riga ya kara da cewa shugabannin jam'iyya na yanzu za su bi duk wata hanya da tsari da doka ta ba su dama wajen hana su Kwankwaso yi masu karfa-karfa.

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“Hakan ba zai yiwu ba. Za mu bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da cewa Kwankwaso bai karɓi tsarin jam’iyyar daga hannunmu ba.”
Shugaban na NDC a Kano ya kuma bayyana cewa ya samu umarni daga shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su dakatar da taron zaɓen shugabanni na jihar.
Ya kara da an ɗauki matakin ne saboda lokacin da Kwankwaso ya shiga jam’iyyar, duk da cewa irin wannan taro ya gudana a wasu jihohi.
A cewarsa:
"An ce mana kada mu yi taron saboda akwai shirin miƙa jam’iyyar ga Kwankwaso. Shi ya sa kuke ganina a nan maimakon wajen taron. Ba za mu bari a take haƙƙin ƴan jam’iyya ba. Za mu yi duk mai yiwuwa domin ba mu goyon bayan zalunci.”
Wannan shi ne karo na farko da Mai Riga ya fito fili ya yi magana bayan shigowar Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, cikin jam’iyyar NDC, kwanaki kaɗan bayan karɓar katin zama ɗan jam’iyya.
A baya, ya fitar da sakon taya murna da maraba ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da mutanensa tare da neman jama'a su mara masu baya.
Makusancin Atiku ya kai NDC kara
A baya, mun wallafa cewa daya daga cikin manyan jam'iyyar ADC, Dr. Umar Ardo ya ce zai ci gaba da shari’a kan sahihancin rajistar jam’iyyar adawa ta NDC.
Ya zargi NDC da rashin cika sharuddan rajista na INEC jim kadan bayan jagororin siyasa irinsu Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun shige ta bayan barin ADC.
Dr. Umar Ardo, wanda tsohon ɗan takarar gwamna a Adamawa ne ya ce ya taba kai ƙarar shugabanni kamar su Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari a baya.
Asali: Legit.ng

