NDC Ta Budewa Obi Ƙofa, Ta Mika Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa ga Kudancin Najeriya
- Jam’iyyar adawa ta NDC ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na zaben 2027 ga yankin Kudancin Najeriya
- Ta yanke wannan hukunci ne jim kadan bayan Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso suka sauya sheka zuwa cikinta
- NDC ta fara shirye-shiryen yadda za ta gudanar da zaben fitar da gwani yayin da ta ke duba yiwuwar amfani da tsarin masalaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Buba Galadima, makusancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jam’iyyar NDC ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ga yankin Kudu.
Ta yanke wannan hukunci ne a lokacin da ake ganin magoya bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi na neman iyayen gidansu su tsaya takara a 2027.

Source: Facebook
Buba Galadima ya bayyana matsayar NDC da suka koma ƙasa da kwanaki biyu da suka wuce a yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, 2026.
NDC na shirin harkokin zaben 2027
Jaridar Daily Post ta ruwaito Buba ya ce jam’iyyar na gab da kammala muhimman shirye-shiryenta na shiga sahun fafatawar siyasa gabanin zaben 2027 mai zuwa.
Injiniya Buba Galadima ya ce NDC za ta miƙa cikakken rajistar ƴaƴanya ga Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya , INEC a ranar 5 ko 6 ga watan Mayu, 2026.
Ya ce wannan mataki ne mai muhimmanci domin tabbatar da sahihancin jam’iyyar a hukumance gabanin harkokin siyasa su kara zafi.m

Source: Facebook
A cewarsa:
"Da zarar mun kammala wannan, komai zai tafi daidai.”
Wannan na nuna cewa jam’iyyar na kokarin cika dukkanin sharuddan da doka ta tanada kafin fara fafatawar zaɓe.
Jam'iyyar NDC za ta fitar da ɗan takara
Game da tsarin fitar da ɗan takara, Buba Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da niyyar ɗaukar tsarin masalaha a yanzu.
Maimakon haka, ya jaddada cewa za a fi karkata ga gudanar da zaɓen fitar da gwani domin bai wa ‘yan takara dama su fafata a bisa tsarin gaskiya.
A ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2026 ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, tare da Kwankwaso, suka sanar da shiga jam’iyyar NDC a hukumance.
Wannan sauya sheƙa ta zo ne bayan ficewarsu daga ADC wacce ta dade tana fama da rikice-rikicen cikin gida, Yayin da Obi ke nuna sha'awar tsaya wa takara.
Rahotanni sun nuna cewa Obi bai halarci wasu tarurrukan ADC ba bayan wani babban taron shugabannin jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Rikici ya kunno wa NDC kai a Kano
A baya, kun ji cewa Shugaban NDC a Kano, Usaini Isa Mai Riga ya ce ba zai miƙa tsarin jam’iyya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kamar yadda ya ce ana ƙoƙarin yi.
Ya bayyana cewa ba a cimma matsaya game da yadda za a tafiyar da NDC ba, kuma ba zai lamunci takun Kwankwaso da mutanensa na shirin kwace jam'iyyar da suka raina ba.
Hon. Usaini Mai Riga ya kuma zargi Sanata Kwankwaso da shigowa tana nuna masu Izza, sannan ya ki sauraron mutanen da ya tarar suna tafiyar da NDC kafin zuwansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


