Yadda Gwamnatin Abba Ta Bayar da Kwangilolin N996.29bn a Kano

Yadda Gwamnatin Abba Ta Bayar da Kwangilolin N996.29bn a Kano

  • Gwamnatin Kano ta ce ta ba da kwangilolin ayyuka na N996.29bn a karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, inda aka kammala ayyuka 867 a fadin jihar
  • Kwamishinan gwamnati ya ce ba a karbo ko sisi a matsayin bashi domin gudanar da ayyukan ba, yayin da aka soke kwangiloli biyar saboda karya yarjejeniya ko rashin kyakkyawan aiki
  • Bayanan gwamnati sun nuna cewa ayyukan sun shafi dukkan kananan hukumomin Kano 44, ciki har da gidaje, hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da ababen more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ba da kwangilolin ayyuka da darajarsu ta kai N996.294bn tun bayan hawan mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda aka kammala ayyuka 867 a fadin jihar.

Gwamnatin ta kuma ce ba ta karbo ko sisi a matsayin bashi, daga cikin gida ko wajen Najeriya, domin daukar nauyin ayyukan da aka aiwatar ba, yayin da aka soke kwangiloli biyar saboda karya yarjejeniya ko rashin kyakkyawan aikin.

Kara karanta wannan

"Ba abu ne mai sauki ba"; Gwamna Abba ya fadi wahalar mulkin Kano

Gwamnatin Abba ta bayar da kwangiloli
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Kwamishinan sayen kayayyaki na gwamnati, bibiyar ayyuka da tantancewa, Nura Maaji Sumaila, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026 a wani taron manema labarai, cewar rahoton jaridar Tribune.

An bayar da kwangiloli a Kano

A cewarsa, kundin bayanan ma’aikatar ya kunshi ayyuka 1,557 da aka rarrabe a fili, wadanda ake aiwatarwa a fadin jihar Kano.

Ya bayyana cewa ayyuka 654, wato 42%, na ci gaba da gudana, yayin da aka kammala ayyuka 867, wato 55.68%.

Kwamishinan ya kara da cewa ayyuka 26, wato 1.66%, suna matakin bayar da kwangila, yayin da ayyuka 10, wato 0.64%, aka tsara su kuma suke jiran bayar da kwangila.

Sumaila ya ce alkaluman sun nuna cewa ana samun gagarumin ci gaba wajen aiwatar da ayyukan, inda aka riga aka kammala fiye da rabin ayyukan.

Yadda Kudaden Ayyukan Suka Kasance

Kwamishinan ya bayyana cewa jimillar kudin kwangilolin ayyukan ta kai N996.294bn, yayin da aka amince da N695.196bn ta hanyar takardar No Objection Certificate (NOC).

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya kawo ruɗani, ya ce yan bindiga sun kai hare hare ƙananan hukumomi 26

Ya ce ma’aikatar ta kuma tantance takardun biyan kudi na ayyuka da suka kai N444.747bn

A cewarsa, kudin da aka amince da shi ta NOC ya kai kusan 69.78% na jimillar kudin kwangilolin, yayin da kudaden da aka tantance suka kai 44.64% na jimillar kudin kwangilolin.

Sumaila ya ce bambancin da ke tsakanin jimillar kudin kwangiloli da kudin da aka amince da shi ta NOC ya kai kusan N301.098bn.

An bayar da kwangiloli a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce akwai kuma bambancin kusan N250.448bn tsakanin kudin da aka amince da shi ta NOC da kudaden da aka tantance domin biyan su.

Kwamishinan ya jaddada cewa alkaluman suna nuna yadda tsarin aiwatar da kudade yake, kuma ya kamata a fahimce su bisa la’akari da ayyukan da ke ci gaba, tsarin tantance takardun biyan kudi da kuma kudaden da gwamnati ke da su.

Abin da gwamnatin Kano ta ce kan auren gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarni ga malamai kan auren gata da ta gudanar.

Gwamnatin ta umarci malaman su yi amfani da wa’azinsu wajen karyata bayanan ƙarya game da shirin aurar da jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng