Ganduje Ya Kara Tsokano Kwankwaso, Ya Kwatanta Shi da 'Tsuntsu' a Siyasar Najeriya

Ganduje Ya Kara Tsokano Kwankwaso, Ya Kwatanta Shi da 'Tsuntsu' a Siyasar Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kira magudun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da “tsuntsun siyasa."

Ganduje ya kira Kwankwaso da wannan suna ne saboda yadda ya ke yawan sauya jam’iyya daga wannan dandali zuwa wani.

Ganduje.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje a masallaci lokacin da ya halarci taron daura aure a Abuja Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Tsohon gwamnan na Kano, Ganduje ya bayyana haka ne yayin wata hira da BBC Hausa a yan kwanakin da suka shige, inda ya tattauna kan siyasar jihar Kano.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

Rabiu Kwankwaso ya sake canza jam'iyya

Kwankwaso, wanda shi ma tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ta baya NNPP zuwa ADC a ranar 30 ga Maris 2026, yana mai danganta matakin da rikicin cikin gida.

Sai dai bayan ‘yan makonni, ya kuma sake sauya sheka zuwa NDC tare da 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi.

Bayanai sun nuna cewa jiga-jigan biyu sun dauki matakin ne bayan hukuncin Kotun Koli da ya shafi rikicin shugabancin ADC, kama

Abin da Ganduje ya ce kan Kwankwaso

Wannan canza jam'iyyar da Kwankwaso ya yi a karshen makon nan, ta sa aka fara dauko kalaman da Ganduje ya yi game da siyasar madugun Kwankwasiyya.

Ganduje ya ce Kwankwaso ya zama 'dan siyasar da ke yawo kamar tsuntsu, yana sauya jam’iyya lokaci zuwa lokaci.

“Ya zama tsuntsun siyasa da ke sauka a kowanne dandali. Muna da dabarun da muka yi amfani da su wajen karbe iko daga hannunsa.”

Kara karanta wannan

Aminu Abdussalam: Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya fice daga jam'iyyar ADC

Tsohon shugaban na APC ya kara da cewa sauya jam’iyya akai-akai na nuna koma baya a siyasar Kwankwaso, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a gidanda da ke jihar Kano Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ganduje ya yi fatali da tasirin ADC

Ganduje ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fahimci matsalolin da ke tunkarar Kwankwaso, wanda hakan ya sa ya yanke shawarar komawa APC domin daidaita siyasar Kano.

Ya ce gwamnan ya bi sahun Gwamnatin tarayya ne domin tabbatar da kwanciyar hankali a jihar.

Dangane da ko ADC za ta zama barazana ga APC, Ganduje ya ce hakan ba zai faru ba, yana mai cewa jam’iyyar na cike da masu ra’ayi daban-daban da ke neman tikitin shugaban kasa.

Kwankwaso ya tura sako ga yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Rabiu Musa Kwankwaso , ya aika da sako ga magoya bayansa bayan shiga jam'iyyar NDC.

Kwankwaso ya buƙaci duk wani mai goyon bayansa a kowane lungu da sako na kasar nan, ya garzaya ya yi rajista da jam’iyyar NDC wadda ya sauya sheka zuwa cikinta.

Madugun Kwankwasiyya da Peter Obi, sun shiga jam’iyyar NDC ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026 bayan sun fice daga jam’iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262