Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dakatar da Wasu Ciyamomin Kananan Hukumomi 3
- Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bebeji, Rogo da Bagwai na tsawon watanni uku saboda zarge-zargen almundahanar kuɗi
- Kakakin majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa kwamitin bincike damar gudanar da aikinsa cikin adalci
- Majalisar ta ce shugabannin na iya rasa kujerunsu idan bincike ya tabbatar da zarge-zargen da ake yi musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kano - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku.
An ce majalisar ta dakatar da ciyamomin kananan hukumomin Bebeji, Rogo da Bagwai daga bakin aikinsu na tsawon watanni uku.

Source: Facebook
An dakatar da ciyamomi 3 a Kano
Mai magana da yawun majalisar dokokin jihar Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya tabbatar da hakan ga wakiliyar Legit Hausa ta wayar tarho a ranar 4 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a
Kamaluddeen Shawai ya ce an yanke wannan hukunci ne a yayin zaman Majalisar, inda aka amince da dakatarwar domin ba da damar gudanar da bincike kan wasu batutuwan da suka shafi gudanar da ayyukansu.
Majalisar Kano ta ce matakin ya zama dole domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da bin ka'idojin shugabanci a matakin kananan hukumomi.
"Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi guda uku, akwai Bebeji, akwai Bagwai akwai Rogo."
- Kamaluddeen Sani Shawai.
Dalilin dakatar da ciyamomin Kano
Kamaluddeen Sani Shawai ya bayyana cewa:
"Kamar yadda aka sani akwai kwamitin da majalisar ta kafa kwanakin baya, wadanda suka zauna domin bibiyar korafe korafen da suka taso daga garuruwan yankunan da wasu kungiyoyi suka kawo a kan su shugabannin kananan hukumomin.
"Kwamitin ya zauna ya ci gaba da bibiyar lamura, kuma a yau sun gabatar da rahoto gaban majalisa, inda duk 'yan majalisar suka amince a dakatar da shugabannin na watanni uku.
"Wannan zai ba da damar a gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge bisa adalci."
Zargen zargen da ake yi wa ciyamomi

Source: Facebook
Mai magana da yawun majalisar dokokin Kanon, ya yi karin haske da cewa ciyamomin da aka dakatar na iya rasa kujerunsu gaba daya idan har aka tabbatar da sun aikata zarge zargen da ake yi masu.
"Wadannan zarge zargen suna da nasaba da almundahanar kudade da kuma kauce ka'idar aiki a gwamnatance.
"Idan har bincike ya tabbatar da wadannan zarge zargen haka suke, to za mu iya cewa za su iya sallama da kujerunsu; idan kuma bincike ya nuna akasin haka, to za su iya dawo wa kujerunsu kamar yadda ka'ida ta tanadar."
- Kamaluddeen Sani Shawai.
Majalisar Kano ta yi sabuwar doka
A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisar Kano ta amince da dokar da za ta takaita yadda makarantu masu zaman kansu ke ƙara kuɗin makaranta a faɗin jihar.
Sabuwar dokar ta wajabta wa makarantu tuntubar ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) kafin ƙara kuɗi, kuma ƙarin ba zai wuce kashi 10 ba.
Dokar ta kuma rage kuɗin harajin da makarantu ke biya ga Hukumar Makarantu Masu Zaman Kansu daga kashi 15 zuwa kashi 5.
Asali: Legit.ng
