Kwastam Ta Faɗi Lokacin da Za Ta Dauki Ma'aikata a 2026, Ta Sauya Tsarinta
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da sababbin sauye-sauye game da tsarin daukar ma'aikata domin inganta ayyukanta
- Kwanturola Janar Adewale Adeniyi ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen maye gurbi cikin lokaci tare da bai wa matasa damar neman aiki akai-akai
- Kwastam ta bayyana cewa an dauki ma'aikata 3,852 a aikin 2024/2025, tana mai cewa tsarin tantancewa da aka gina zai sa daukar ma'aikata ya fi sauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da babban sauyi a tsarin daukar ma'aikata wanda zai kawo ci gaba ga hukumar.
Kwatsam ta bayyana cewa daga yanzu za ta rika gudanar da daukar sababbin ma'aikata kowace shekara maimakon jira tsawon lokaci kafin sake bude daukar aiki.

Source: Twitter
An fitar da sunayen masu neman aikin Kwastam
Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja, cewar Punch.
Haka ya biyo bayan fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma'aikatan shekarar 2024/2025.
Ya ce an bullo da wannan tsari ne domin samar da ingantaccen shirin tsara ma'aikata, wanda zai bai wa hukumar damar maye gurbin jami'an da suka yi ritaya cikin gaggawa tare da bai wa matasan Najeriya damar samun damar shiga aikin gwamnati akai-akai.
A cewarsa, hukumar ta daina amfani da tsohon tsarin da masu neman aiki ke shafe shekaru suna jiran sake bude daukar ma'aikata kafin su sake samun wata dama.

Source: Facebook
Kwastam: Za a bude shafin daukar ma'aikata
Adeniyi ya bayyana cewa ana sa ran bude daukar ma'aikatan shekarar 2026 daga baya a wannan shekara, kuma hakan zai kasance karkashin sabon tsarin da za a rika aiwatarwa duk shekara.
Ya ce Hukumar Kwastam ta riga ta samar da cikakken tsarin tantance masu neman aiki, hanyoyin bincike da kuma matakan tabbatar da sahihanci, wanda zai sa daukar ma'aikata a nan gaba ya kasance cikin sauki da inganci.
Ya ce:
"Hukumar Kwastam ta Najeriya tana komawa tsarin daukar ma'aikata na shekara-shekara. Daukar ma'aikata ba zai kasance wani abu da ake yi bayan shekaru da dama ba. Zai zama tsari na dindindin da za a gudanar kowace shekara.
"Za a bude daukar ma'aikatan shekarar 2026 daga baya a bana, kuma burina shi ne a kammala dukkan matakan daukar ma'aikatan cikin shekara guda, daga sanarwa har zuwa fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara."
Adeniyi ya bayyana cewa jinkirin da aka samu a aikin daukar ma'aikatan 2024/2025 ya samo asali ne saboda gina cikakken tsarin da zai rika tallafawa daukar ma'aikata a shekaru masu zuwa, cewar Daily Post.
A cewarsa:
"Tsarin tantancewa da tabbatar da sahihanci da aka gina yayin wannan aiki yana nan, kuma ba sai an sake gina shi ba. Jinkirin da aka samu a wannan karon ya kasance sakamakon gina wannan tsari, kuma yanzu an riga an kammala hakan."
Ya bayyana cewa sabon tsarin daukar ma'aikata na shekara-shekara zai amfani hukumar da kuma masu neman aiki, domin zai inganta tsarin tsara ma'aikata tare da rage rashin tabbas da matasa ke fuskanta wajen jiran bude daukar aiki.
Adeniyi ya ce hakan zai bai wa hukumar damar tsara maye gurbin ma'aikatan da suka yi ritaya ko suka bar aiki tun kafin a samu gibin ma'aikata.
Ya kuma ce sabon tsarin zai bai wa wadanda ba su yi nasara ba damar sanin lokacin da za a sake bude daukar ma'aikata domin su sake shiri ba tare da dogon lokaci na jiran sanarwa ba.
Kwastam ta rage harajin shigo da kaya
An ji cewa shugaban hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) Adewale Adeniyi ya sanar da cewa an rage harajin shigo da gwanjon motoci kashi 15 zuwa kashi 5 cikin 100.
Adeniyi ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin majalisar wakilai a Abuja yayin da yake kare kasafin kudin NCS na 2026.
Shugaban kwamitin Leke Abejide ya yaba wa gwamnatin Tinubu akan wannan matakin da ya ce zai saukaka wa al'umma.
Asali: Legit.ng


