2027: Sauya Shekar Kwankwaso da Obi zuwa NDC Ya Rikita Siyasar Najeriya
- Sauya shekar da jagororin siyasa a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi ya jawo rikita-rikita a siaysar Najeriya ana gab da fara gangamin siyasa
- Manyan siyasar biyu sun tattare magoya bayansu daga jam'iyyar hamayya ta ADC bayan rikicin shugabanci da ke neman hana ruwa gudu a hadakar yan adawa
- Ana tsoron wannan sauya sheka zai girgiza siyasar 2027 da ke tafe yayin da 'yan adawa suka rabu a kan kokarin fitar da APC daga mulkin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa
FCT Abuja - Sauya sheƙar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya girgiza siyasar Najeriya.
A ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu na shekarar 2027 ne Peter Obi da Kwankwaso suka tattara magoya bayansu daga ADC zuwa NDC yayin da ake shirin fafutukar zaben 2027.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa jagororin biyu sun gana da shugaban NDC, Seriake Dickson, a Abuja inda bayan tattaunawa mai tsawo aka ba su katin zama 'yan jam’iyyar.
Yadda Kwankwaso da Obi suka sauya sheka
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hotuna da bidiyo daga wajen taron sun nuna yadda Kwankwaso da Obi suka halarci rajistar zaben kai tsaye.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan barkewar rikici a ADC, su biyun ke tattaunawa da NDC da kuma PRP domin neman sabuwar mafakar siyasa.
Sai dai bayan hukuncin Kotun Kolin Najeriya na baya-bayan nan da ya mayar da rikicin shugabancin ADC zuwa kotun ƙasa, sun yanke shawarar ficewa.
Majiyoyi sun ce sun zaɓi NDC ne saboda sabuwar jam’iyya ce da ba ta da rikice-rikicen shugabanci irin wanda suka fuskanta a ADC.

Source: Facebook
Haka kuma, akwai fargaba a PRP kan yiwuwar sababbin matsaloli bayan wata ƙungiya ta bayyana kanta a matsayin shugabanci.

Kara karanta wannan
"Za mu yi cikakkiyar biyayya": NDC ta mika sakonni ga Kwankwaso bayan sauya sheka
Ana kuma zargin cewa suna shirin tsayawa takara tare a tafiyarsu ta OK movement wanda ka iya zama wata siyasa da za ta yi babban tasiri a Najeriya.
Dalilin sauya shekar jagororin ADC
Bincike ya nuna cewa rikicin cikin gida, rashin daidaito da kuma rashin fayyace batun rabon tikitin shugaban ƙasa ne suka sa Obi da Kwankwaso suka yanke shawarar barin ADC.
Majiyoyi sun bayyana cewa jam’iyyar ta kasa bayyana matsayinta kan ko tikitin shugaban ƙasa zai koma Arewa ko Kudu, lamarin da ya janyo rashin gamsuwa.
Wata majiya shaida wa jaridar cewa:
“An ɗauke mu a matsayin sababbin shiga, ba kamar waɗanda suka kafa jam’iyyar ba, kuma hakan bai yi mana daɗi ba.”
Malam Jabir Ibrahim Yaro, shugaban OK movement a Abuja ya shaidawa Legit cewa sun bar ADC ne saboda akwai fargabar za a yi masu 'kafa a shari'ar da za a ci gaba da yi.
Ya ce:
“Kuma dukanmu mun san mutanen da ke bayan duk rikice-rikicen da ke cikin jam’iyyun adawa, har da ADC.”
"Idan ka duba sabon hukuncin Kotun Ƙoli, ya kamata ka fahimci cewa tarko ne. Wannan ra’ayina ne na kaina. Ba ni lauya ba ne, amma tarko ne domin Kotun Ƙoli ta mayar da shari’ar zuwa Kotun Tarayya ta Ƙoli.”
“Kuma ka san wa ke da iko da Babbar Kotun. Kin san abin da ke faruwa a ɓangaren shari’a a ƙasar nan.”
NDC ta yi wa Kwankwaso da Obi maraba
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NDC a Kano ta aika sakonni ga jiga-jigan siyasa a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi bayan sun sauya sheka zuwa cikinta ranar Lahadi 3 ga Mayu, 2026.
Haka kuma ta aika sako na daban ga Kwankwaso wanda ta bayyana da uba a siyasar Najeriya, musamman Kano inda ta bayyana cewa za ta zama mai cikakkiyar biyayya ga jagoran Kwankwasiyya.
Shugaban jam'iyyar reshen jihar Kano, Hon Husaini Isah Mai Riga ya kuma yi magana game da rabon madafun iko a NDC tare da nanata cewa dukkanin al'amarinsu na cikin gida na su ne kadai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

