Aminu Abdussalam: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Ya Fice daga Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar ADC reshen jihar Kano ta samu koma baya bayan babban jigo a cikinta ya sanar da yin murabus ba tare da wani bata lokaci ba
- Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya sanar da barin jam'iyyar ADC wadda bai dade da sauya sheka zuwa cikinta ba
- Duk da ficewarsa daga ADC, tsohon mataimakin gwamnan ya aika da sakon godiya ga shugabannin jam'iyyar bisa goyon bayan da aka ba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi murabus daga jam’iyyar ADC mai adawa.
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Mayun 2026.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa an aika wasikar ne zuwa ga shugaban ADC na ƙaramar hukumar Gwarzo da ke jihar Kano.
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bar ADC
A cikin wasiƙar, tsohon mataimakin gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.
Ya danganta matakin nasa da abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa kwanan nan da kuma buƙatar sake duba zamansa a jam’iyyar domin ya dace da hangen nesansa na siyasa.
“Wannan shawarar ta zo ne bayan dogon tunani da kuma tuntuɓar abokan huldar siyasa, magoya baya, da masu fatan alheri a faɗin jihar."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Meyasa ya bar jam'iyyar ADC?
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ƙara da cewa sauye-sauyen da ake samu a yanayin siyasa sun sa ya zama dole a gare shi ya samar wa kansa sabuwar hanyar siyasa, jaridar PM News ta kawo rahoton.
“Abubuwan da ke faruwa a siyasa kwanan nan da sauye-sauyen da ake samu a yanayin siyasa sun sa ya zama dole na sake duba mambancina don amfanin jama’a da kuma makomar jiharmu da ma ƙasa baki ɗaya."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Ya bayyana cewa matakin nasa ya samo asali ne daga abin da ya siffanta da kishin ƙasa da kuma sha’awar bin hanyar siyasa da ta yi daidai da manufofinsa.
“Shawarar tawa ta ginu ne a kan kishin ƙasa da kuma buƙatar bin hanyar siyasa da ta dace da hangen nesa na na shugabanci nagari, dabi’un dimokuradiyya, da kuma ci gaba mai dorewa na jiharmu mai daraja."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Source: Facebook
Gwarzo ya yi godiya ga shugabannin ADC
Tsohon mataimakin gwamnan, ya godewa shugabanni da mambobin jam’iyyar saboda goyon bayan da ya samu a lokacin zaman sa a cikinta.
“Ina so na nuna matuƙar godiyata ga shugabanni da mambobin jam’iyyar saboda haɗin kai, girmamawa, da goyon bayan da na samu a lokacin zama na a jam’iyyar."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Aminu Abdulsalam Gwarzo bai bayyana matakin da zai dauka a gaba a siyasance ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, amma murabus ɗin nasa na iya samun alaƙa da sauye-sauyen siyasa da ake yi a halin yanzu gabanin babban zaɓen 2027.
ADC ta magantu kan ficewar Kwankwaso, Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta tanka bayan ficewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi.
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi bayyana ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar a matsayin koma-baya, amma ba babban rauni da zai ruguza ta ba.
Bolaji Abdullahi ya amince cewa ficewar tasu koma-baya ce, amma ya dage cewa ba babban rauni ba ne ga manufofin ADC.
Asali: Legit.ng


