An Yaye daga ADC, 'Yan Majalisa 17 Sun Bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC
- Kwanaki kadan bayan sauya shekar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi, wasu daga cikin yan majalisar wakilai sun bi bayansu
- 'Yan majalisar wakilai 17 ne suka sauya sheka daga hadakar yan adawa ta ADC da aka hada a kwanakin baya zuwa NDC
- Ana ganin wannan babban sauyi zai kara girgiza rikon da jam'iyyar APC da ke mulkin Najeriya a majalisa yayin da zabe kr kuratowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Aƙalla 'yan majalisar wakilai 17 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa NDC, a wani mataki da ke ƙara sauya fasalin siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027.
An bayyana sauyin sheƙar ne a hukumance a zauren majalisar wakilai yayin zaman ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026 inda shugabannin majalisar suka karanta wasiƙun sauyin jam’iyyar da ‘yan siyasar suka aike.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan lamari ya biyo bayan sauyin sheƙa da ya faru a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu na shekarar 2026.
Manyan 'yan siyasa sun bar ADC
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, suka fice daga ADC zuwa NDC.
Sauyin nasu Obi da Kwankwaso ya ƙara ɗaukar hankali a fagen siyasa, domin ana kallon su a matsayin manyan jiga-jigan da za su taka muhimmiyar rawa a fafatawar zaɓen 2027.
Haka kuma, a yayin zaman majalisar, an sanar da cewa Leke Abejide shi ma ya sauya sheka daga ADC zuwa jam’iyyar APC, abin da ke nuna yadda ADC ke fuskantar raguwar ƙarfi a majalisar.
Daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheka zuwa NDC akwai Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, da Peter Aniekwe.
'Yan majalisar da suka koma ADC
Sauran sun haɗa da Mukhtar Zakari, George Oluwande, Munachim Umezuruike, Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da kuma Abdulhakeem Ado.

Source: Facebook
Wannan jerin sun nuna cewa sauyin sheƙar ta shafi yankuna daban-daban na ƙasar, lamarin da ke nuna yiwuwar NDC na ƙoƙarin gina ƙarfi a matakin ƙasa baki ɗaya.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan sauyin jam’iyya na iya sauya Majalisar wakilai, musamman idan aka yi la’akari da yadda jam’iyyun ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinsu kafin zaɓen 2027.
NDC: Kwankwaso da Obi sun rikita siyasa
A baya, mun wallafa cewa sauya shekar da jagororin siyasa a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi ya jawo rikita-rikita a siaysar Najeriya ana gab da fara gangamin siyasa.
Manyan siyasar biyu sun tattare magoya bayansu daga jam'iyyar hamayya ta ADC bayan rikicin shugabanci da ke neman hana ruwa gudu a hadakar yan adawa da ke adawa da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
Ana tsoron wannan sauya sheka zai girgiza siyasar 2027 da ke tafe yayin da 'yan adawa suka rabu a kan kokarin fitar da APC daga mulkin Najeriya tare da sauya lissafin siyasar kasa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

