Ana Korafi a kan Zargin Lakadawa Musa Mai Sana'a Duka kan Tallan Tinubu a Katsina
- An ce Musa Mai Sana’a, ya sha da kyar daga hannun wasu fusatattun matasa a Jihar Katsina, bayan ya yi yunkurin tallata Shugaba Bola Tinubu
- Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da matsalar tsaro da rashin jin dadin jama'a ke kara tsananta a wasu sassan Arewa maso Yamma
- Sai dai tsohon minista, Solomon Dalung, ya ce duk da rashin amincewa da sakon Mai Sana'a, bai kamata matasa su yi yunkurin lakada masa duka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Katsina – Ana zargin fitaccen jarumin Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya sha da kyar daga hannun wasu fusatattun matasa a Jihar Katsina, bayan da ya isa jihar da niyyar tallata Shugaba Bola Tinubu.
An ce lamarin ya faru ne a kofar shiga garin Katsina, inda ake da wata alama mai rubuce da “Barka da zuwa jihar Katsina”.

Source: Facebook
Dalung ya wallafa a Facebook cewa ana zargin jarumin ya hau kan wurin ne da nufin yin wani bidiyo na tallata Tinubu, amma wasu matasa da ke wurin suka gargade shi da ya sauko.
Dalilin fusatar matasan
A cewar bayanan da aka wallafa kan lamarin, matasan sun nuna rashin amincewarsu da yunkurin yin tallan Tinubu a wurin, inda suka bukaci Musa Mai Sana’a ya dakatar da abin da yake yi.
Daga bisani lamarin ya rikide zuwa tashin hankali, inda aka ce matasan sun yi yunkurin lakada masa duka.
An ce jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da ceto jarumin daga hannun matasan, yayin da ake cewa ya bar hularsa a wurin a lokacin da yake gudun tsira.
Dalung ya yi gargadi
Tsohon minista kuma dan siyasa, Solomon Dalung, ya yi Allah-wadai da yunkurin dukan jarumin, yana mai cewa Musa Mai Sana’a na da damar goyon bayan Tinubu da yin yakin neman zabensa.
Dalung ya bayyana cewa mutanen da ba su amince da sakon Musa ba ma suna da damar kalubalantar abin da yake fada, amma bai kamata hakan ya koma tashin hankali ba.
Ya ce matasan Katsina ya kamata su bari jarumin ya yi magana, sannan su gabatar masa da tambayoyi masu muhimmanci kan halin da ake ciki a kasar.
“Me ya canza? Me ya faru da alkawuran da aka yi kan tsaro? Me zai sa wani ya yarda cewa karin shekaru hudu za su kasance daban?”
Dalung ya bayyana tambayoyin da ya kamata a yi.
Ya ce irin wadannan tambayoyi za su fi yin tasiri wajen isar da sakon rashin amincewa da gwamnati fiye da amfani da karfin tsiya.

Source: Twitter
Matsalar da Tinubu zai fuskanta
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Dr Femi Alabi, ya koka kan rashin isasshen wayar da kan jama'a game da shirye-shiryen gwamnatin tarayya tare da yada bayanan da ba daidai ba.
Alabi ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bude taron kaddamar da masu kula da yakin neman zaben Tinubu/Shettima na jihohi da aka gudanar a Abuja.
Jigon na APC ya ce ingantaccen shugabanci ya kamata ya tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun zama sauye-sauye da jama'a za su iya gani a rayuwarsu.
Asali: Legit.ng

