ADC Ta Fadi Hanyar da Za Ta Zabi dan Takarar Shugaban Kasa bayan Ficewar Kwankwaso da Obi
- Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta zaɓi ɗan takarar shugaban kasa ta hanyar amfani da tsarin maslaha domin zaben 2027
- Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana wannan shirin ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2027
- Bayanan na Abdullahi sun fito ne sa’o’i kaɗan bayan ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga ADC zuwa sabuwar jam’iyyar NDC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta bayyana tsarin da za ta yi amfani da shi wajen zabar dan takararra na shugaban kasa a zaben 2027.
Jam'iyyar ADC ta ce ɗan takararta na shugaban ƙasa na 2027 zai fito ne ta hanyar maslaha, inda ta tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta da isasshen lokacin da za ta ɓata.

Source: Facebook
Sakataren yada labarai na jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.
Meyasa ADC za ta yi amfani da maslaha
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa za a yi amfani da tsarin maslaha ne saboda babu lokacin batawa wajen gudanar da zaben fitar da gwani.
“Za mu yi amfani da tsarin maslaha ne saboda, kamar yadda kai (Charles) ka faɗa daidai, babu damar gudanar da zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato."
- Bolaji Abdullahi
Wannan matakin ya biyo bayan ficewar tsofaffin gwamnonin Anambra da Kano, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, waɗanda suka bar ADC suka koma jam'iyyar NDC.
Kakakin ADC ya soki wasu 'yan siyasa
Kakakin na ADC ya ci gaba da bayar da hujjar cewa wasu ’yan siyasa sun fi damuwa da samun tikitin jam’iyya fiye da tsarin akidun da ke siffanta ƙungiyoyin siyasa.
“Suna jiran a miƙa musu tikiti ne kawai. Idan ka ce kana son tsayawa takara a zaɓe, kuma ka yarda da batun sauya ƙasa, ya kamata ka san abin da jam’iyyarka ke wakilta.”
- Bolaji Abdullahi
Jam'iyyar ADC ta ragargaji Peter Obi
Bolaji Abdullahi ya kuma soki Peter Obi kan abin da ya kira rashin nuna sha’awa ga tsarin akidar jam’iyyar.
“Mun kafa kwamitin tsara manufofi wanda ya yi aiki na kusan wata biyu zuwa uku don samar da tsare-tsaren da ke fayyace abin da za mu yi daban."
"Kuna iya gayyatar Mai girma Peter Obi nan ku tambaye shi, mece ce matsayar ADC kan tallafin mai? Mene ne tsarin ADC kan tsaro? Bai sani ba, domin bai taɓa nuna sha’awa ba.”
- Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
Peter Obi ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NDC kwanan nan, matakin da ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da sauya fasalin siyasa gabanin zaɓubbuka masu zuwa.
Aminu Gwarzo ya fice daga ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya raba gari da jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya tabbatar da murabus dinsa daga jam'iyyar ADC a cikin wata wasika da ya aikawa shugabanta na karamar hukumar Gwarzo.
A cikin wasikar, tsohon mataimakin gwamnan ya nuna godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar kan irin goyon bayan da suka ba shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

