Buba Galadima Ya Gayyaci Atiku zuwa NDC bayan Sauya Shekar Kwankwaso da Obi

Buba Galadima Ya Gayyaci Atiku zuwa NDC bayan Sauya Shekar Kwankwaso da Obi

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC bayan sun raba gari da da ADC
  • Jigo a NDC, Buba Galadima, ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tayin shigowa sabuwar jam'iyyar
  • Buba Galadima ya yi gargadin cewa idan Atiku bai shiga jam'iyyar ba, za a dora masa alhakin kasa hada kan 'yan adawa

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani babban jigo a sabuwar jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, shawara.

Buba Galadima ya bukaci Atiku Abubakar, da ya shiga jam’iyyar NDC, inda ya yi gargadin cewa za a iya dora masa alhakin gazawar hadaka kan 'yan adawa gabanin babban zaben 2027.

Buba Galadima ya bukaci Atiku ya shigo NDC
Buba Galadima da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Hon Saifullahi Hassan, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PRP ta yi magana kan sauya shekar Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Atiku Abubakar ya samu tayin shiga NDC

Ya bayyana cewa nasara ko gazawar kokarin kafa hadaka da ake yi a halin yanzu zai dogara ne kacokan kan ko manyan masu fada aji a harkar siyasa, ciki har da Atiku, sun amince su marawa sabuwar jam'iyyar baya.

Buba Galadima ya bayyana cewa tuni alkiblar siyasa ta fara karkata zuwa ga wani dandamali na hadakar adawa, inda fitattun mutane da dama suka riga suka shiga cikin NDC.

“Gaskiyar lamarin ita ce Peter Obi da Kwankwaso sun koma NDC; sun kawo hadin kan adawa ne domin kayar da Tinubu."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya ba Atiku shawara

Buba ya bukaci Atiku da ya bi wannan tafarkin, inda ya jaddada cewa hadin kai shi ne kadai sahihiyar hanyar da za a iya fuskantar gwamnati mai ci.

“Wannan ne ya sa nake kiran tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya biyo mu kamar yadda muka bi shi... ta yadda za a samu hadin kan adawa don kayar da wannan gwamnatin."

Kara karanta wannan

Martanin jam'iyyar ADC bayan ta rasa Kwankwaso da Peter Obi zuwa NDC

“Idan ya ki, za a dora wa Atiku alhakin rugujewar wannan tafiya ta siyasa gabanin 2027."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya ba Atiku shawara
Buba Galadima na jawabi a wajen taro tare da su Sanata Kwankwaso Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jam'iyyar NDC na kara karfi a Najeriya

A cewarsa, yawancin fitattun ’yan adawa tuni suka fara tururuwa zuwa NDC, wanda hakan ya sa ta zama babban sansanin hadin kai gabanin zagayen zabe mai zuwa.

“Gaskiyar ita ce dukkan manyan 'yan siyasa yanzu suna cikin NDC, kuma duk wata shakka na kin shiga zai iya raunana damar da hadakar take da ita."

- Buba Galadima

Buba Galadima ya kara da cewa zama a wajen wannan hadakar na iya yin tasiri ga burin siyasar Atiku, ciki har da damarsa a zaben 2027.

Atiku zai shilla zuwa Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai kai ziyara zuwa kasar Amurka.

Atiku zai kai ziyarar ne domin jawo hankalin duniya kan taɓarɓarewar tsaro, halin ƙuncin tattalin arziƙi, da kuma faduwar darajar shugabanci a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku ya ce Najeriya tana fuskantar cikakken rikicin cikin gida wanda ba za a iya ci gaba da raina shi ko mayar da shi batun siyasa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng