Jam'iyyar PRP Ta Yi Magana kan Sauya Shekar Kwankwaso da Obi zuwa NDC
- Shugaban jam'iyyar PRP, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana kan yadda 'yan siyasa ke yawan sauya sheka gabanin zaben 2027
- Hakeem Baba-Ahmed ya yi karin haske kan yadda Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka koma NDC maimakon jam'iyyarsa ta PRP
- Hakan na zuwa ne yayin da 'yan adawa ke ta sauya sheka zuwa jam'iyyu daban-daban domin neman takara da fatan samun mulki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar ba ta cikin wani matsin lamba na jawo Peter Obi ko Rabiu Musa Kwankwaso duk da matsayin da suke da shi a matsayin jiga-jigan ‘yan adawa.
Hakan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun hada kai sun fita daga ADC sun koma jam'iyyar NDC maimakon PRP.

Source: UGC
Batun kin shigar Kwankwaso PRP
Daily Trust ta wallafa cewa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi bayanin ne yayin da yake magana a wata tattaunawa kan yiwuwar shigar manyan ‘yan siyasar biyu cikin PRP.
Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar ba ta da wata damuwa kan shawarar da suka dauka ta rashin shiga PRP, kuma tana girmama zabinsu na siyasa.
“Game da Peter Obi da Kwankwaso, ba mu da wata matsala da rashin shigowarsu jam’iyyarmu. Muna musu fatan alheri duk inda suka dosa,”
In ji shi.
Me yasa ake sauya sheka a yau?
Baba-Ahmed ya nuna cewa karancin lokaci kafin manyan harkokin zaɓe na iya zama wani dalili ga ‘yan siyasar da ke tunanin sauya jam’iyya.
“Ku duba, lokaci ya yi karanci sosai ga wadanda suka fahimci tsauraran jadawalin da ke gaban masu sauya jam’iyya. Lokaci ya yi kadan sosai domin mutum ya koma daga wata jam’iyya zuwa wata,”

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
In ji shi.

Source: Facebook
Duk da kin nuna gaggawa wajen jawo manyan ‘yan siyasa, shugaban PRP ya ce jam’iyyar na samun karin masu sha’awar shiga daga sassa daban-daban na Najeriya.
“Muna samun mutane da yawa da ke shigowa jam’iyyarmu kuma muna matukar farin ciki da hakan. Mu jam’iyya ce ta akida. Mun shafe rayuwarmu gaba daya muna yin abin da ya dace,”
In ji shi.
Vanguard ta wallafa cewa a yanzu haka tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a LP, Datti Baba-Ahmed ya koma PRP, inda ya ce ba neman shugabanci ba ne ya kai shi jam'iyyar.
Bala Mohammed ya sauya sheka
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APM.
Bala Mohammed ya bayyana cewa zai yi takarar Sanata a zaben 2027 domin samun damar cigaba da yi wa jama'ar jihar Bauchi aiki.
Yayin wata hira da aka yi da shi, gwamnan ya bayyana cewa sun sauya shekar ne bayan rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar adawa ta PDP.
Asali: Legit.ng
