'Ina N4tr Suka Shiga"? Atiku Ya Kalubalanci Tinubu kan Farfado da Matatun Mai
- Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da dora wa gwamnatocin baya alhakin matsalar matatun man fetur na Najeriya duk da shi ne a mulki
- 'Dan takarar shugaban kasa a ADC ya ce gwamnatin yanzu ta kamata ta yi bayani kan makudan kudin da aka kashe wajen gyaran matatun
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bashin da matatun man Fatakwal, Warri da Kaduna ke bin NNPCL ya karu zuwa Naira tiriliyan 8.67 a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan yadda gwamnatinsa ke alakanta matsalolin matatun man fetur mallakar gwamnati da gwamnatocin da suka gabata.
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu, wadda ta wa lhaji Atiku Abubaka fiye da shekaru uku a mulki, ba za ta iya ci gaba da dora mata alhakin matsalolin da ta gada ba, musamman ganin yadda aka kashe makudan kudade a kan matatun.

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa kan harkokin sadarwar jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2026.
Atiku ya tuhumi Tinubu
A ruwayar Vanguard, Atiku ya kafa hujjojinsa ne kan alkaluman kudi da ke cikin bayanan Kamfanin Mai na Kasa NNPCL, inda ya ce bashin matatun Fatakwal, Warri da Kaduna da ke kan NNPCL ya karu daga kusan Naira tiriliyan 4.52 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 8.67 a 2024.
Ya ce karin da ya kai kusan Naira tiriliyan 4.15 cikin shekara guda ya kamata ya sanya gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan kudin da aka kashe da kuma abin da jama'a suka samu a madadinsu.
Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, ya kuma yi tsokaci kan kalaman babban jami'in gudanarwa na NNPCL, Bayo Ojulari, da ya ce ana asara ne kawai a matatun.
Ojulari ya bayyana hakan ne a watan Fabrairun 2026 yayin wani taro a taron makamashi na kasa da kasa da aka gudanar a Abuja.
Ojulari ya yi fallasa, cewar Atiku
Atiku ya ce wannan ikirari ya fallasa abin da ya kira sabani a yadda gwamnatin tarayya ta gabatar da shirin gyaran matatun a baya.

Source: Facebook
A kalamansa:
“NNPCL ya sanar da cewa matatun na aiki da kashi 70 cikin 100 na karfinta, tare da bayyana hakan a matsayin nasarar da aka samu a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.
“Yanzu da murna ta koma abin kunya, wannan gwamnati tana son ’yan Najeriya su yarda cewa matatun man basussuka ne kawai da aka gada daga gwamnatocin baya.”
A ranar 26 ga Nuwamban 2024, NNPCL ta sanar da cewa tsohuwar matatar Port Harcourt mai karfin tace ganga 60,000 a rana ta koma aiki, inda ta ce manyan motoci sun fara dibar fetur, dizal da kananzir.
Atiku ya gana da tawagar Birtaniya
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya gana da babban jami'in diflomasiyyar Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu na neman 'ƙaryata' rahoton da ƙasar Amurka ta fitar kan Najeriya
Tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da ake ciki a Najeriya a halin yanzu, kamar yadda dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 ya bayyana a wani sako da ya fitar bayan zaman.
Ganawar ta zo ne yayin da Birtaniya ke kara tuntubar shugabannin siyasa da jami'an zabe gabanin babban zaben 2027 da ake dab da gudanarwa tare da bayar da tabbacin ci gaba da sa ido kan batun.
Asali: Legit.ng

