Pantami Ya Girgiza APC a Gombe, Ya Samu Goyon Bayan Sanata Haruna Garba
- Tsohon Sanatan Gombe ta Arewa, Ambasada Haruna Garba, ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Pantami, tare da mika masa cikakken tsarin siyasar sa
- Haruna Garba ya umarci magoya bayansa da su mara wa Pantami baya tare da hada kai da shi domin zaben 2027 da kuma bayan haka
- Sanatan ya ce ayyukan Pantami a mukaman da ya taba rike wa, da kuma kwarewarsa a harkokin cikin gida da na kasa da kasa, ne suka sa ya goyi bayansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Tsohon Sanatan Gombe ta Arewa, Ambasada Haruna Garba, ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
A cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya fitar a madadin tafiyar Pantamiyya a ranar Litinin, an bayyana cewa Haruna Garba ya kuma umarci magoya bayansa da su hada kai da Pantami domin cin zaben 2027.

Source: Facebook
Sanarwar da Pantami ya fitar a Facebook ta ce Haruna Garba ya yi hakan ne saboda yadda yake ganin kyawawan ayyukan Pantami a mukaman gwamnati da ya rike a baya.
Dalilin goyon bayan Pantami
A cewar sanarwar, Haruna Garba ya bayyana cewa Pantami ya samu nasarar sauya wasu hukumomi daga halin kusan durkushewa zuwa zama daga cikin wadanda suka fi kwarewa a Najeriya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa dangantakar Pantami da manyan mutane da hukumomi a duniya wata babbar dama ce ga Najeriya baki daya, ba wai Gombe kadai ba.
An ce Pantami ya taba zama shugaban Global ICT and Digital Ministers, inda ya jagoranci ministocin fasahar sadarwa da tattalin arzikin zamani sama da 193 daga shekarar 2022 zuwa 2023.
Karin bayanin Haruna Garba
Haruna Garba ya ce Pantami ya tabbatar da kasancewarsa mutum mai gaskiya da rikon amana a cikin gwamnati da wajen gwamnati.
A cewar sanarwar, zaben Pantami bisa gaskiyarsa, amana, rikon alkawari, kwarewa, dangantakarsa ta cikin gida da kasa da kasa, da kuma iliminsa, zai kasance abu mai kyau ga Gombe da Najeriya.
Daga karshe, tsohon sanatan ya mika cikakken tsarin siyasar sa ga Pantami tare da neman mambobin tsarin su yi aiki tare da shi.

Source: Facebook
Matsayin Haruna Garba a Gombe
Haruna Garba ya wakilci Gombe ta Arewa a Majalisar Dattawa daga shekarar 2003 zuwa 2007. Daga baya ya zama Ambasadan Najeriya a Kuwait daga 2012 zuwa 2015.
Ya kuma kasance mai neman takarar gwamnan Gombe a zaben 2019, sannan ya rike mukamin Babban Akanta na farko na Jihar Gombe da kuma kwamishinan kudi.
Sanarwar ta bayyana Haruna Garba a matsayin daya daga cikin fitattun masu taimakon jama'a da Gombe ta taba samarwa, tana mai cewa ya taimaka wa mutane da dama a fannoni daban-daban.
Za a sake fadar sarkin Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Jihar Gombe ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangila tare da mika wuraren aikin sake fasalin Fadar Sarkin Gombe.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa ana sa ran kammala ayyukan, wadanda ake gudanarwa karkashin JPDA, cikin watanni shida.
Daraktan-Janar na JPDA, Mahmood Yusuf ya bukaci dan kwangilar da ya gudanar da aikin bisa ka'idojin da aka tanada a cikin takardun kwangilar.
Asali: Legit.ng

