Kwankwasiyya na Duba Yiwuwar Haɗaka da NDC, PRP bayan Hukuncin Kotun Koli

Kwankwasiyya na Duba Yiwuwar Haɗaka da NDC, PRP bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana yadda ta ke kallon hukuncin kotun kolin Najeriya a kan rikicin shugabancin jam'iyyar ADC
  • Kwanaki biyu bayan hukuncin, Kwankwasiyya ta bayyana cewa tana nazari tare da duba yiwuwar sabuwar haɗakar siyasa
  • Ƙungiyar ta ce hukuncin ya ƙara masu kwarin gwiwa kan adalci a tsarin shari’ar kasar nan, amma duk da haka tana duba batun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ƙungiyar Kwankwasiyya ta fitar da sanarwa ga ‘yan Najeriya da magoya bayanta kan hukuncin da kotun koli ta yanke dangane da rikicin shugabanci a jam’iyyar ADC.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar, ƙungiyar ta yaba da yadda kotun ta nuna jajircewa da gaskiya a wajen yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Martanin Nafi'u Bala ga hukuncin kotun koli game da shari'ar rikicin ADC

Kwankwasiyya ta fitar da sanarwar kan hukuncin kotu
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a cikin magoya baya a wani taro a Kano Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Twitter

A sakon da ta wallafa a shafinsa na Facebook, kungiyar ta yadda da kotun inda ta soke wasu umarni da ta ce sun jawo rudani a cikin jam’iyyar.

Kwankwasiyya ta yabi hukuncin kotu

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa akwai fatan bangare shari'ar kasar nan zai yi abin da ya dace wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

Ta ce: "Mun lura da jarumta da kuma fayyace gaskiya da Kotun koli ta nuna wajen soke umarnin da ba su dace ba, waɗanda suka haifar da rashin tabbas a cikin jam’iyyar.”

Ƙungiyar ta bayyana cewa hukuncin ba wai nasara ce ga bin doka kawai ba, har ila yau ya sake jaddada muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen tabbatar da daidaito a cikin al’umma mai dimokuraɗiyya.

Sanarwar ta ƙara da cewa hukuncin ya aika da saƙo mai ƙarfi cewa ba za a iya amfani da shari’a wajen tayar da rikici ko rushe tsarin siyasa na gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Mark da Nafi'u Gombe: Kotun Koli ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Duk da cewa kotun ta mayar da shari’ar zuwa ƙaramar kotu domin ci gaba da sauraro, Kwankwasiyya ta ce tana da yakinin cewa wannan hukunci zai zama ginshiƙi na adalci, gaskiya da kammala shari’ar yadda ya dace.

Kwankwasiyya na duba yiwuwar hadaka

Ƙungiyar ta ce a wannan lokaci mai muhimmanci, tana nazarin hukuncin sosai domin fahimtar tasirinsa, musamman ganin ƙarancin lokaci kafin zaɓen 2027.

Ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin kauce wa duk wani tarko na siyasa ko na shari’a da zai iya hana jagoranta da sauran ‘yan adawa shiga zaɓe yadda ya kamata.

A cewar sanarwar, ƙungiyar na duba duk wasu hanyoyi na doka da dabaru, ciki har da yiwuwar haɗin gwiwa da wasu jam’iyyu kamar NDC da PRP domin kare dimokuraɗiyya da muradin jama’a.

Ta jaddada cewa manufarta ita ce kare haƙƙin siyasa da tabbatar da cewa babu wani yanayi da aka ƙirƙira da zai hana miliyoyin ‘yan Najeriya samun wakilci mai inganci.

Kwankwasiyya na duba yiwuwar haɗaka da wasu jam'iyyu
Obi, Kwankwaso, Tambuwal, David Mark, Aregbesola, Atiku da jiga-jigan haɗakar a zanga-zangar da suka yi a Abuja Hoto: Rabi'u Musa kwankwaso
Source: Facebook

Da ya ke zantawa da Legit, Mansur Umar Kurugu, mai magana da yawun Kwankwasiyya na II ya ce hukuncin alama ce cewa har yanzu adalci na aiki a ƙasar.

Kara karanta wannan

Wike/Turaki: Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar shugabancin jam'iyyar PDP

Ya ce:

“Wannan ya ƙara mana ƙwarin gwiwa a kan tsarin shari’armu.”
“Yana nuna cewa har yanzu akwai cibiyoyi a ƙasar nan da ba sa sayar da mutuncinsu da ƙimarsu.”

Sai dai ya soki hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), inda ya zarge ta da nuna son kai, yana mai cewa ana ƙoƙarin hana ‘yan adawa damar tsayawa takara.

Jigo a Kwankwasiyya ya bar ADC

A wani labarin, mun wallafa cewa fitaccen jagora a tafiyar Kwankwasiyya, Kabiru Adamu Abdullahi ya fice daga jam'iyyar haɗakar adawa da ADC a Kano.

Ya bayyana cewa ya bar ADC a lokacin da ake raɗe-raɗin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da tawagarsa za su bar jam'iyyar zuwa NDC kafin zaben 2027.

Hon. Kabiru Adamu Abdullahi ya bayyana cewa wannan barin jam'iyya da ya yi umarnin jagora ne, sannan ya yi wa ADC fatan alheri da godiya da aka ba shi dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng