Martanin Nafi'u Bala ga Hukuncin Kotun Koli game da Shari'ar Rikicin ADC

Martanin Nafi'u Bala ga Hukuncin Kotun Koli game da Shari'ar Rikicin ADC

  • Nafi’u Bala da ke da'awar shi ne shugaban ADC ya mayar da martani ga mutanen David Mark da ke murna game da hukuncin kotun koli
  • Ya bayyana cewa kotun koli ta kori karar da tsagin David Mark ya shigar, yana mai ikirarin shi ne ya yi nasara bayan an umarci a koma kotun ƙasa
  • Kotun koli ta mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya domin a ci gaba da sauraren batun shugabancin jam'iyyar adawa ta ADC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala, ya bayyana cewa babu wata nasara da David Mark da mabiyansa suka samu a hukuncin da kotun koli ta yanke.

A ranar 30 ga watan Afrilu, shekarar 2026, ne kotun koli ta kori karar da tsagin David Mark a ya shigar yana kalubalantar matsayin shugabanci a jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Da gaske an haramta wa jam'iyyar ADC tsayar da 'yan takara a zaben 2027? An samu bayani

Nafiu Bala ya kafe a kan shi ne shugaban ADC
Nafiu Bala a lokacin da ya ke zanga-zangar adawa da tsagin David Mark a Abuja Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa sai dai rahotanni sun nuna cewa kotun ta kuma mayar da shari’ar zuwa gaban babbar kotun tarayya domin a ci gaba da sauraron ta.

Sai dai a bangare guda, Kotun koli ta rusa hukuncin da aka yi na cewa ADC ta koma yadda ake ciki kafin yanzu, lamarin da INEC ta fassara da daina yarda da su David Mark.

ADC: Nafi'u Bala ya soki David Mark

Da yake mayar da martani a hirarsa da DCL, Nafi’u Bala ya nace kan cewa har yanzu shi ne shugaban ADC na kasa.

Hon Nafiu Bala ya bayyana cewa:

"Amma a doka, har gobe ni ne shugaban ADC a tarayyar Najeriya. "Kotu ta kori kararsu, saboda haka ni ne na yi nasara."

A cewarsa, umarnin da kotun ta bayar na a ci gaba da shari’a a kotun kasa bai sauya gaskiyar cewa shi ne ke rike da shugabancin jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnan Bauchi zai sauya sheka, ya fida kujerar da zai nema a 2027

Ya fassara hukuncin kotun a matsayin wanda ke karfafa matsayinsa, na cewa shi ne jagora a jam'iyyar da ta hada yan adawa.

Martani Nafi'u Bala ga shirin INEC

A wani bangare, Nafi’u Bala ya karyata rahotannin da ke cewa hukumar zabe mai zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta amince da David Mark a matsayin shugaban ADC.

Nafiu Bala ya zargi tsagin David Mark a da karya
Nafi'u Bala mai adawa da tsagin David Mark a ADC Hoto: Nafi'u Bala
Source: Facebook

Ya ce wannan batu ba gaskiya ba ne, yana mai zargin cewa tsagin da ke biyayya ga David Mark na yada labaran ƙarya domin yaudarar jama’a da kuma neman kwace ikon jam’iyyar.

Nafi'u Bala ya kara da cewa:

"Ba gaskiya ba ne cewa INEC za ta mayar da sunan David Mark a matsayin shugaban ADC."

Ya zargi bangaren Mark da kokarin rikitar da al’amura saboda matsin lamba da suke fuskanta, yana mai cewa suna kokarin kame jam’iyyar karfi da yaji.

A cewarsa, su ne halastattun ‘yan jam’iyyar ADC, yayin da ya bayyana bangaren David Mark a matsayin wasu ‘yan haɗaka da suka fito daga wasu jam’iyyun da suka ruguje.

Jigon ADC ya yabi hukuncin kotu

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya na duba yiwuwar haɗaka da NDC, PRP bayan hukuncin kotun koli

Adnan Mukhtar, tsohon ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kano kuma mamba a jam’iyyar ADC, ya shaidawa Legit , ya ce yana da kyakkyawan fata game da makomar jam’iyyar duk da rashin tabbas da ake ciki.

Ya ce:

“Wannan babban ci gaba ne ga ƙasa. Kamar yadda kuka sani, ADC ita ce kaɗai jam’iyyar adawa da ke da ƙwazo wajen ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ‘yan Najeriya a faɗin ƙasar na murna.
“Mutane suna farin ciki. Wannan wani kira ne na faɗakarwa ga ADC da ta yi abin da ya dace ta hanyar tsayar da ‘yan takara nagari, ƙwararru kuma masu cancanta a zaɓen gama gari na 2027 mai zuwa."

Ya bayyana fatan ADC za ta yi abin da ya dace wajen tabbatar da an fatattaki APC daga mulki a 2027.

INEC ta yi hukunci kan rigimar ADC

A baya, mun wallafa cewa kotun koli ta yanke hukunci kan shari'ar da ake yi dangane da rigimar shugabancin jam'iyyyar ADC mai adawa da APC da ke mulkin Najeriya.

Hukuncin da kotun kolin ta yanke ya soke wanda kotun daukaka ta zartar wanda ya sa hukumar INEC daina amincewa da shugabancin ADC karkashin David Mark.

Biyo bayan hukuncin na Kotun Koli, INEC ta sauya matsayar da ta dauka kan shuganancin ADC yayin da jam'iyyu ke kokarin gyara matsayarsu da hukumar zaben.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng