Wike/Tanimu: Kotun Koli Ta Raba Gardama kan Shari'ar Shugabancin Jam'iyyar PDP
- Kotun koli ta raba gardama game da shari'ar da ake yi tsakanin ƴaƴan jam'iyyar PDP wanda ya kawo rigima mai tsanani a Najeriya
- A yau Alhamis 30 ga watan Afrilun 2026, Kotun ta yi watsi da karar daukaka kara da tsagin PDP karkashin jagorancin Taminu Turaki ya shigar
- Alkalin kotun koli, Mai shari’a Stephen, ya ce taron PDP da aka gudanar a Ibadan ya saba wa hukuncin baya na babbar kotun tarayya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun koli ta yi zama a shari'ar da ake yi kan rikicin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya da ya ki ci ya ki cinyewa.
Kotun ta yi watsi da karar daukaka kara da kwamitin gudanarwar PDP karkashin jagorancin Taminu Turaki ya shigar.

Source: Twitter
Rikicin PDP: Hukuncin da Kotun koli ta yi
Rahoton Channels TV ya ce an yi hukuncin ne kan karar da kwamitin ya shigar kan rikicin shugabancin jam’iyyar da ake ganin ya lalata tasirin jam'iyyar wurin adawa a Najeriya.
Yayin shari'ar da aka gudanar a Abuja, kotun ta tabbatar da cewa karar ba ta da inganci da ta cancanci goya mata baya.
Mai shari’a Stephen wanda ya karanta hukuncin mafi rinjaye ya bayyana cewa taron kasa na PDP da aka gudanar a Ibadan ranar 15 da 16 ga Nuwamba ya saba doka.
Kotun ta ce an gudanar da taron ne duk da akwai hukuncin babbar kotun tarayya da Mai shari’a James Omotosho ya yanke tun farko kan rikicin cikin jam’iyyar.
Alkalan kotun koli sun soki bangaren Turaki saboda komawa wata kotu mai matsayi iri daya domin neman sabon umarni maimakon su shigar da daukaka kara kai tsaye.

Source: Facebook
Dalilin watsi da karar tsagin Turaki
Kotun ta bayyana matakin a matsayin cin zarafin tsarin shari’a, tana gargadin cewa duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci sakamakon abin da ya aikata, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ta ce:

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotun Koli ta sanya lokacin yanke hukunci kan takaddamar shugabancin ADC
“Masu ɗaukaka ƙarar ba su je kotun ɗaukaka ƙara ba, sai dai sun tafi wata kotu mai matsayi iri ɗaya... Dole ne a bi umarnin kotu kuma suna nan har sai an soke su. Ko da kuwa umarnin ya dace ko bai dace ba, ko ma ya kasance karkatacce.”
Hukuncin ya tabbatar da cewa karar da bangaren Tanimu Turaki ya shigar ba ta da cancanta, saboda haka kotun koli ta yi watsi da ita gaba daya.
Tsohon gwamna ya fadi dalilin barin PDP
A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya sanar da ficewarsa daga babbar jam’iyyar adawa PDP.
Mimiko ya ce ficewar ta fara aiki daga ranar 10 ga Afrilu, 2026 yayin da PDP ke ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da ADC mai adawa a kasar.
Olusegun Mimiko ya bayyana cewa ya bayyana matsayarsa ne bayan tambayoyi da ake yi masa game da zama a PDP mai adawa a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng
