Ana tsaka da Shan Amarci, Amarya Ta Saka Guba a Abincin Ango
- Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 19 bisa zargin yunƙurin kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba a abinci
- An ce matar, Aisha Musa, wadda ta yi aure kimanin kwanaki 40 da suka wuce, ta sanya wani abu da ake zargin guba ne a cikin abincin mijinta
- ‘Yan sanda sun ce sun kama matar bayan samun rahoton lamarin, yayin da aka garzaya da mijin asibiti inda yake samun kulawa kuma halin da yake ciki ya daidaita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta sanar da kama Aisha Musa, wata matar aure mai shekaru 19, bisa zargin yunƙurin kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba a abinci.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Gwamma da ke ƙaramar hukumar Bauchi a ranar 12 ga Agusta 2026.

Source: Facebook
Batun sa guba a abinci
A cewar sanarwar rundunar, wadda Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya fitar a Facebook, matar ta shafe kusan kwanaki 40 da aure.
An ce da misalin ƙarfe 3:15 na rana, matar ta sanya wani abu da ake zargin guba ne a cikin abincin mijinta.
Daga bisani, da misalin ƙarfe 7:40 na dare, wata mata mazauniyar yankin Wuntin Dada ta sanar da ‘yan sanda game da lamarin.
An garzaya da mijin asibiti
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda na Tafawa Balewa Estate suka garzaya wurin domin ɗaukar matakin gaggawa.
Rundunar ta ce an kwashi wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin samun magani.
A cewar ‘yan sandan, wanda abin ya shafa yana samun kulawa a asibitin kuma halin da yake ciki ya daidaita.
Me aka samu a wajen matar?
Rundunar ta ce jami’anta sun kama wadda ake zargin, inda ta yi wata sanarwa bayan an yi mata tambayoyi tare da gargadinta.
An kuma ce an samu kwalbar da babu komai wadda ake zargin an yi amfani da ita wajen ɗauke da gubar fiya-fiya, tare da ragowar abincin da aka samu a matsayin hujjoji.
An tura binciken zuwa SCID
Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a tura lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jiha, SCID.
Rundunar ta ce za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, sannan a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Source: Original
‘Yan sanda sun yi kira ga jama’a
Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da doka da oda a fadin jihar.
Ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Dan majalisa ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Saleh Hodi, ya yi murabus daga kujerarsa ta wakiltar mazabar Disina.
Hodi ya yi murabus ne domin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukumar Shira a zaɓen da ke tafe a jihar Bauchi.
Kakakin Majalisar, Abubakar Sulaiman, ne ya sanar da murabus ɗin a zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce majalisar ta samu wasiƙar Hodi da ke sanar da ita matakin da ya ɗauka.
Asali: Legit.ng

