Sanata Ya Bijirewa Gwamna, Ya Yi Fatali da Zabin Wanda Zai Gaje Shi a 2027
- An fara samun matsala a siyasar jihar Yobe bayan Sanata daga jihar ya yi watsi da ɗan takarar gwamna da wasu shugabannin APC suka goyi baya
- Sanata Ibrahin Mohammed Bomai ya ce zaɓen Baba Wali da aka yi ba matsayar dukkan masu ruwa da tsaki ba ce, illa ra’ayin mutum guda
- Bomai ya bayyana cewa duk wani yunƙurin kakaba ɗan takara ya saɓa wa dimokuraɗiyya, yana mai alƙawarin kare haƙƙin jama’ar Yobe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Sanatan Yobe ta Kudu, Ibrahim Mohammed Bomai, ya fito fili ya bayyana matsayarsa kan zabin wanda zai gaji gwamnan jihar.
Sanata Bomai ya ƙi amincewa da ɗan takarar gwamna da wasu jiga-jigan APC suka zaɓa domin zaɓen shekarar 2027 a jihar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Facebook na sanatan a yau Juma'a 1 ga watan Mayun shekarar 2026.
Sanata ya kalubalanci matakin Gwamna Buni
Bomai ya bayyana cewa matakin da aka ɗauka bai nuna adalci ga jama’ar Yobe ba, yana mai cewa tsarin ya saɓa wa muradun dimokuraɗiyya.
A baya dai wani taron jiga-jigan APC a Yobe ya ayyana Baba Wali, tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, a matsayin wanda suke son ya tsaya takarar gwamna.
Taron ya haɗa da Gwamna Mai Mala Buni da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Ibrahim Geidam, bayan wata ganawa da suka yi a Abuja.
Sai dai Bomai ya bayyana cewa ɗora Baba Wali a matsayin ɗan takara hari ne kai tsaye kan ƙa’idodin dimokuraɗiyya da hakkokin jama’a.
Ya ce shawarar ba ta fito daga dukkan masu ruwa da tsaki na APC ba, illa matakin mutum guda da aka ɗauka ba tare da yardar jama’a ba.

Source: Twitter
Babban abin da sanatan ke zargin Gwamna Buni
Sanatan ya ce abin damuwa ne yadda mutum guda zai rinjayi shugabancin miliyoyin jama’a ba tare da bin ƙa’ida ko mutunta ra’ayin al’umma ba.
Bomai ya ƙara da cewa Yobe mallakin jama’arta ne, ba na wasu tsirarun mutane ba, saboda haka dole shugabanci ya wakilci muradin talakawa.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su kare tsarin dimokuraɗiyya tare da tabbatar da gaskiya, haɗin kai da shugabanci mai riƙon amana a jihar.
Sanatan ya jaddada cewa zai ci gaba da kare haƙƙin jama’a cikin lumana, yana mai cewa ba zai yarda da tsoratarwa ko wariya ba.
Sanata ya yi wa Gwamna Buni kara
An ji cewa jim kadan bayan Gwamna Mai Mala Buni ya nuna wanda ya ke son ya gaji kujerarsa, wani sanata ya yi masa kara a siyasar jihar.
Sanatan Yobe ta Gabas, Mustapha Musa, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan ya nemi kujerarsa ta sanata a 2027.
Mustapha Musa ya janye daga takarar 2027 tare da marawa Gwamna Buni baya a matsayin magajinsa a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

