Faka Faka: Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Ministan Gidaje a Fadar Aso Rock

Faka Faka: Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Ministan Gidaje a Fadar Aso Rock

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin ministan gidaje da raya birane a fadar shugaban ƙasa, Abuja
  • Darma, wanda tsohon shugaban asusun PTDF ne, ya maye gurbin Ahmed Dangiwa ne sakamakon ɗan garambawul da shugaban ƙasa ya yi
  • Yayin tantance shi, sabon ministan ya sha alwashin magance matsalar ƙarancin gidaje da ta addabi sama da 'yan Najeriya miliyan 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon ministan gidaje da Raya Birane a hukumance.

Taron rantsuwar ya gudana ne a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Juma'a, 24 ga Afrilu, 2026.

Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje
Shugaba Bola Tinubu yayin rantsar da Dr. Muttaqha Darma a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Majalisa ta amince da nadin ministan gidaje

Kara karanta wannan

Mummunan iftila'i ya fada wa Amurka, gari guda ya rushe, an rufe sansanin sojoji

Darma ya sami amincewar majalisar dattawa ne a ranar Alhamis bayan tantancewar da aka yi masa sakamakon wasikar neman amincewa da Tinubu ya aika wa Godswill Akpabio, in ji rahoton Punch.

Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dattawa lokacin tantance shi, Dr. Darma ya bayyana cewa:

"Zan yi aiki kafada-da-kafada da majalisar tarayya domin shawo kan matsalar karancin gidaje a Najeriya, musamman idan aka yi la'akari da cewa sama da mutane miliyan 100 ba su da ingantattun gidaje."

Ya kuma gabatar da wasu dabaru da yake son yin amfani da su wajen inganta shugabanci a ma'aikatar gidaje, samar da gidaje cikin sauki da kuma karfafa alaka da sauran hukumomi.

Tinubu ya nada Darma, ministan gidaje

Shugaba Tinubu, a cikin takaitaccen bayani da ya yi yayin taron rantsuwar, ya taya Dr. Darma murna tare da bayyana shi a matsayin "gwani a harkar gidaje."

Shugaban ya jaddada cewa kasar Najeriya na bukatar mutum mai hazaka kamar Darma, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen ci gaban kasa.

Babban mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya wallafa sanarwar rantsarwar a shafinsa na X, inda ya ruwaito Tinubu ya na cewa:

Kara karanta wannan

Muttaqa Darma: Sabon Ministan da Tinubu ya nada ya san matsayarsa bayan tantance shi a majalisa

"Kana da nasaba mai kyau. A matsayin shugaba, muna bukatar kwararru kamar ka.
"Babu tantama cewa ka samar da sakamakon da ake bukata a dukkan ayyukan da ka yi a baya, don haka, an sanya kwarya a burminta."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Kwarewa da ayyukan Darma na baya

Darma ya maye gurbin Ahmed Dangiwa ne, wanda ya bar kujerar sakamakon garambawul din da shugaban kasa ya gudanar a ranar Talata.

Dr. Muttaqha Darma ya sha alwashin magance matsalar gidaje yayin da ya zama minista.
Shugaba Bola Tinubu ya na gaisawa da sabon ministan gidaje, Muttaqha Darma. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Dr. Muttaqha Darma fitaccen masani ne kuma kwararre a fannin ci gaban kasa, wanda ke dauke da digirin digirgir (PhD) a fannin injiniyanci da kasuwanci.

Kafin wannan nadi, ya taba rike mukaman kwamishinan ayyuka da gidaje a jihar Katsina, sannan ya kasance shugaban asusun PTDF tsakanin 2008 zuwa 2012.

Majalisa ta amince da nadin Muttaqha Darma

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Majalisar dattawan ta Najeriya ta tabbatar da Muttaqha Rabe Darma matsayin Minista bayan ta tantance shi da ta yi.

Da yake magana gaban majalisa, Darma ya ce salonsa zai mayar da hankali ne kan dinke gibin jagoranci wanda ya kawo cikas ga samar da gidaje masu inganci a faɗin ƙasar.

Darma ya yarda da girman ƙalubalen ƙarancin gidaje a Najeriya, amma ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a iya magance shi da ingantattun manufofi da jajircewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com