Ana Jiran Hukuncin Kotu: David Mark Ya Fadi abin da Zai Faru da ADC a Zaben 2027

Ana Jiran Hukuncin Kotu: David Mark Ya Fadi abin da Zai Faru da ADC a Zaben 2027

  • Shugaban ADC, David Mark, ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa za su fafata a dukkan zabukan shekarar 2027 duk da shari’a da ke gaban kotu
  • Mark ya bayyana hakan ne bayan wani hukunci da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke, wanda ya haramta wa INEC amincewa da zabubbukan jam'iyyar
  • Tuni lauyoyin jam’iyyar ADC suka fara shirin daukaka kara da kuma neman dakatar da aiwatar da hukuncin kotun har sai abin da shari'ar gaba ta nuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, ya kwantar wa mambobin jam’iyyar hankali game da makomar jam’iyyar adawar a zabukan 2027.

David Mark, wanda ya yi magana a daren Laraba bayan karbar bayani daga lauyoyin jam’iyyar, ya ce babu dalilin fargaba game da kararrakin da ake yi.

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

David Mark ya bayyana cewa ADC za ta shiga dukkan zabukan 2027
Shugaban ADC na kasa, David Mark na jawabi ga mambobin jam'iyyar a Abuja. Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

"Za a ga ADC a zabe" - David Mark

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da Bolaji Abdullahi, sakataren watsa labaran jam'iyyar ADC na kasa ya fitar a shafinsa na X.

Ya jaddada cewa jam’iyyar ADC za ta bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin ganin ta samu cikakkiyar nasara a kotu gabanin zaben.

Sanata Mark ya bayyana cewa:

“Ina so in tabbatar muku cewa za mu yi nasara a dukkan shari’un da ake yi, kuma sunanmu zai kasance a cikin takardar kuri’a a kowane zabe.
"Ko da yake ni ba lauya ba ne, zan jagoranci wannan fafatawa daga gaba, kuma lallai za mu yi nasara.”

Hukuncin kotu da matakin jam’iyyar ADC

Wannan tabbaci na Sanata Mark ya zo ne jim kadan bayan da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin hana hukumar INEC amincewa da duk wani taro da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ya shirya.

Kara karanta wannan

2027: An kunna rikici a PRP da ke shirin kawar da Tinubu, ADC ta magantu

Kotun ta kuma hana David Mark da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya katsalandan a ayyukan zababbun shugabannin jam’iyyar na jihohi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sai dai jam’iyyar ADC ta bayyana cewa lauyoyinta sun riga sun fara shirin daukaka kara kan wannan hukunci, tare da neman kotu ta dakatar da aiwatar da shi har sai an kammala sauraren karar.

Shirye-shiryen zaben 2027

Shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki na neman tabbatar wa mambobinsu cewa jam’iyyar na nan daram kuma tana ci gaba da shirye-shiryen babban zaben 2027.

Wannan dambarwa ta shari’a tana zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke kara kaimi wajen shirya wa zabukan 2027.

David Mark ya bukaci mambobin jam’iyyar da su kasance masu kwarin gwiwa, inda ya ce jam’iyyar tana da duk abin da ake bukata domin shawo kan kalubalen shari’ar da take fuskanta.

ADC tsagin David Mark, ta jaddada cewa za ta warware dukkan shari'o'in jam'iyyar.
Wasu daga cikin shugabannin 'yan adawa a Najeriya a karkashin jam'iyyar ADC. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kotun Koli za ta yi hukunci a shari'ar ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam'iyyyar ADC ta tsinci kanta cikin rikicin shugabanci wanda ya sanya shari'a ta kai har zuwa ga Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Rurum ya samu goyon baya domin maye gurbin Kawu Sumaila a Majalisar Dattawa

Kotun Koli ta sanya lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar wadda ta shafi bangaren David Mark da Nafiu Bala Gombe.

Tun da farko dai bangaren David Mark ya bukaci kotun da ta yanke hukunci kan shari'ar domin kada hakan ya jawo masu matsala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com