'Amurka na Tattauna Batun Jefa Bama Baman Nukiliya Iran'
- Tsohuwar ‘yar majalisar Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta yi ikirarin cewa manyan jami’an Amurka na gudanar da tattaunawa kan yiwuwar amfani da nukiliya a Iran
- Greene ta ce Amurka na duba yiwuwar rage matakin da ake bukata kafin a yi amfani da makaman nukiliya, duk da ikirarin Donald Trump na cewa ya yi nasara
- Tsohuwar ‘yar majalisar ta yi wannan ikirarin ne a wani sakon da ta fitar a ranar Lahadi, ba tare da gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin nata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Tsohuwar ‘yar majalisar wakilan Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta yi gargadin cewa Amurka na iya fuskantar mummunan sakamako idan ta dauki matakin amfani da makaman nukiliya a yakin da take yi da Iran.
Greene ta yi ikirarin cewa ana gudanar da manyan tarukan dabarun yaki domin tattauna yiwuwar amfani da makaman nukiliya a kan Iran.

Source: Getty Images
Anadolu ta ruwaito cewa Greene ta bayyana cewa ba zato kawai take yi ba, tana mai cewa ta san cewa irin wannan tattaunawa na gudana, tare da bayyana matakin a matsayin abin da ya saba wa dabi’un bil’adama.
Ta rubuta a shafinta na X cewa:
“Ba zato nake yi ba, na sani. Kuma wannan mummunan aiki ne.”
Greene ta zargi gwamnatin Amurka da yin watsi da wasu rahotannin leken asiri na cikin gida da ke nuna cewa Iran ba ta kusa kera makamin nukiliya, tana mai cewa gwamnati ta fi karkata ga ikirarin Isra’ila.
Gargadin amfani da nukiliya
Greene ta ce yakin da ake yi ya janyo wahalhalun fararen hula masu yawa, tare da taimakawa wajen bai wa Iran iko kan wasu muhimman hanyoyin samar da makamashi a yankin.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wani karin dagula rikicin zai iya haifar da abin da ta kira babban rikici a duniya, wanda zai iya janyo durkushewar tattalin arziki da kuma asarar rayuka da ba a taba ganin irinsa ba.
Greene ta kara da cewa tarihi zai daura alhakin duk wani rikicin nukiliya kan shugabannin da suke kan madafun iko a halin yanzu.
Fadar White House ba ta mayar da martani nan take kan bukatar samun karin bayani game da ikirarin tsohuwar ‘yar majalisar ba.

Source: Getty Images
Iran na son kama sojin Amurka
A wani bangare na rikicin, rundunar sojin Iran ta sanar da bayar da tukuicin da ya kai dalar Amurka 30,000 ga duk wanda ya kashe ko ya kama wani sojan Amurka.
Shugaban Rundunar Sojin Iran, Amir Hatami, ya ce an tsara shirin ne bayan samun “buƙatu masu yawa” daga mutanen da ke son shiga cikin shirin samun kudi kan batun.
Magana kan Hormuz
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta yi watsi da ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump na cewa mashigar Hormuz za ta kasance mallakar Amurka nan ba da jimawa ba.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce mashigar Hormuz ta kasance karkashin ikon Iran kuma za ta ci gaba da kasancewa haka, yana mai cewa rufe ko bude mashigar zai kasance karkashin umarnin Iran.
Gharibabadi ya ce ba za a iya kwace mashigar Hormuz ta hanyar rubutu a X, jirgin dakon jiragen yaki ko umarnin shugaban kasa ba, yayin da Trump ya ce bayan Amurka ta yi galaba a kan Iran.
Asali: Legit.ng

