2027: Jigon APC Ya Fadi Abubuwan da za Su Zama Matsala ga Tinubu

2027: Jigon APC Ya Fadi Abubuwan da za Su Zama Matsala ga Tinubu

  • Jigon APC, Dr Femi Alabi, ya ce yaɗa bayanan ƙarya da kuma karancin wayar da kan jama’a na barazana ga nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Alabi ya ce matsin tattalin arziki da rashin ingantaccen tsarin sadarwa na iya hana ganin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu
  • Ya bayyana hakan ne a Abuja a ƙarshen mako, yayin bikin rantsar da masu kula da harkokin jam’iyyar APC a jihohi na Tinubu/Shettima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Wani jigon jam’iyyar APC, Dr Femi Alabi, ya yi gargadin cewa yaɗa bayanan ƙarya da gibin sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a na iya yin illa ga tafiyar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Alabi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen bikin rantsar da masu kula da harkokin jam’iyyar a jihohi domin tabbatar da nasararTinubu/Shettima a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan faduwar APC a Osun, Tinubu ya tura muhimmin sako ga Ademola Adeleke

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa 'yan Najeriya bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta ruwaito cewa an gudanar da taron ne a Abuja kan taken “Inganta shugabanci da cgaba: Rawar da ‘yan kasa za su taka”.

Abin da zai ba Tinubu matsala

Alabi ya ce duk da cewa ingantaccen shugabanci ya dogara ne kan rikon amana, bunƙasar tattalin arziki, samar da abubuwan more rayuwa da kuma bin doka, gibin sadarwa na ci gaba da zama babban kalubale.

Ya ce yaɗa bayanan ƙarya, rashin jituwa a siyasa, rashin aikin yi ga matasa, karancin shiga harkokin farar hula da kuma rashin isasshen wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen gwamnati na iya kawo cikas ga nasarorin da ake kokarin samu.

"Karkatar da bayanan gaskiya, rashin jure ra'ayin hakuri a harkokin siyaa, rashin aikin yi a tsakanin matasa, karancin sa hannun 'yan kasa a al'amuran yau da kullum, da kuma karancin ankarar da jama'a kan shirye-shiryen gwamnati za su iya zama zagon kasa ga kokarin da ake yi.,"

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

In ji Alabi.

Ya bukaci ‘yan kasa da su daina kasancewa masu kallon siyasa daga gefe kawai, tare da kira ga sababbin masu yada manufofin gwamnati da su kasance masu hada gwamnati da jama’a cikin gaskiya da mutunci.

Alabi ya ce ya kamata a gudanar da wayar da kan jama’a a matakin karkara cikin gaskiya, ladabi, mutunta ra’ayoyi daban-daban da kuma bin ka’idojin dimokuradiyya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a taron APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma yi kira da a kara hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, kungiyoyin fararen hula da al’ummomin yankuna domin tabbatar da ingantacciyar sadarwa.

Martanin shugaban kungiyar

A nasa bangaren, Mai kula da kungiyar ta kasa, Dr Dominic Alancha, ya bukaci shugabannin kungiyar a matakin jihohi da su fara kai rahoton ayyukan gwamnatin Tinubu zuwa ga al’ummomin karkara.

Leadership ta wallafa cewa Alancha ya ce matakin ya zama wajibi musamman a yayin da ake fara samun sababbin kawance-kawance na siyasa gabanin babban zaben 2027.

Nasarar Adeleke a Osun

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaben gwamnan jihar Osun a matsayin tabbacin cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da bunkasa a Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, bayan Adeleke ya samu nasara a zaben da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta.

Shugaban ya ce ya kira Adeleke domin taya shi murnar nasarar, yana mai cewa sakamakon zaben ya nuna irin amincewar da al’ummar Osun suka nuna masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng