Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Sa Gwamnoni da Dama Za Su Sha Kunya a Zaben 2027

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Sa Gwamnoni da Dama Za Su Sha Kunya a Zaben 2027

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnonin da ke tunanin za su yi amfani da magudin zaɓe da ikon hukumomin jihohi domin ci gaba da mulki bayan 2027 za su sha kunya
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da tabarbarewar ayyukan gwamnati na iya shafar yadda masu zaɓe za su kada ƙuri’unsu
  • Kwankwaso ya ce ’yan Najeriya na ƙara wayewa a siyasance kuma za su iya ƙin zaɓen gwamnonin da ke neman komawa kan kujerunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na National Democratic Congress (NDC), ya yi magana kan gwamnoni dangane da zaben 2027.

Kwankwaso ya ce gwamnonin da ke tunanin za su yi amfani da magudin zaɓe da ikon hukumomin jihohi domin ci gaba da mulki bayan 2027 za su sha kunya.

Kara karanta wannan

'Ba su da sauran mamora a siyasa': Kwankwaso ya ce ta karewa su Ganduje a Kano

Kwankwaso ya yi magana kan gwamnoni
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya kasance baƙo a shirin tattaunawa da manyan mutane na News Agency of Nigeria (NAN) a Abuja ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026.

Kwankwaso ya soki wasu gwamnoni

Tsohon gwamnan na Kano ya ce wasu gwamnonin da suka gaza magance matsalolin al’ummomin da suke jagoranta suna sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bisa zargin cewa suna ganin yin hakan zai taimaka musu wajen sake lashe zaɓe.

Ya ce ƙara nuna rashin gamsuwa da matsalolin rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da raguwar ingancin ayyukan gwamnati na iya yin tasiri kan shawarar masu zaɓe a rumfunan zaɓe, The Punch ta kawo labarin.

A cewar Kwankwaso, ’yan Najeriya na ƙara wayewa a siyasance, kuma za su iya ƙin gwamnonin da sauran ’yan siyasar da ke neman wani wa’adi duk da cewa suna da iko kan tsarin gwamnati.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso ya ce kan INEC bayan taya Adeleke murnar tazarce a Osun

“Abin da nake hasashen zai faru a zaɓen 2027 shi ne, yawancin gwamnonin da ke neman sake zaɓe za su sha kunya saboda mutane ba za su mara musu baya ba,” in ji shi.

Ya ambaci ilmi da rashin tsaro

Kwankwaso ya ce ’yan Najeriya na da hujjoji masu ƙarfi na neman ingantacciyar gwamnati, yana mai ambaton yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma illar rashin tsaro ga al’ummomi a faɗin ƙasar.

Ya tuna cewa a lokacin da yake gwamnan Kano, gwamnatinsa ta bai wa ilimi fifiko ta hanyar faɗaɗa damar samun ilimin firamare, sakandare da manyan makarantu ga mazauna jihar da suka cancanta.

Ya kuma ce gwamnatinsa ta aiwatar da shirye-shiryen magance ƙalubalen Almajiri tare da zuba jari a gine-ginen makarantu, ciki har da dakunan kwanan ɗalibai.

A cewarsa, wannan ƙwarewa ta nuna cewa gwamnati za ta iya inganta rayuwar ’yan ƙasa matuƙar ta tsara yadda za ta yi amfani da albarkatun da take da su yadda ya kamata.

Kwankwaso ya soki wasu gwamnoni
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya soki masu sauya sheka zuwa APC

Kwankwaso ya kuma soki yadda ’yan siyasa ke ƙara sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa APC, yana mai bayyana hakan a matsayin yunƙurin da wasu ’yan siyasa ke yi domin samun moriyar siyasa gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun

Sai dai ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa a ƙarshe masu zaɓe ne za su yanke hukuncin sakamakon zaɓen.

Dalilin Kwankwaso na yin aiki da Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sanya ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027.

Kwankwaso ya ce ya amince da zama abokin takarar Peter Obi a zaben 2027 ne saboda bukatar daidaiton kasa, adalci da kawo sauyin dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng