"Mulki na Allah ne": Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Hakura da Neman Kujerar Sanata Ndume
- Mataimakin kakakin majalisar dokokin Borno, Abdullahi Musa Askira ya janye daga takarar Sanatan Kudancin yankin
- Ya bayyana cewa ya hakura ne bayan jam'iyya mai mulki ta APC ta amince ta sake mara wa Sanata Ali Ndume baya don ya koma majalisa
- Abdullahi Musa Askira ya kuma aika sako ga magoya bayansa daga yankin Borno ta Kudu, inda ya ce mulki daga Allah
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdullahi Musa Askira, ya janye daga takararsa ta Sanatan Borno ta Kudu.
Wannan ya kara tallafawa takarar da Sanata Ali Muhammad Ndume karo na biyar, wanda a halin yanzu shi ne ke wakiltar yankin a majalisar dattawa.

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa wannan mataki ya zo ne bayan shugabanni da jiga-jigan APC daga kananan hukumomi tara na Borno ta Kudu sun amince baki daya da Ndume a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar a zaben 2027.
An mara wa takarar Ali Ndume baya
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa magoya bayan jam’iyyar sun kuma hada sama da Naira miliyan 40 domin sayen fam din takarar sanata ga Ndume.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Bilyaminu Ngulde, ya fitar, Askira ya tabbatar da cewa ya fice daga neman takarar baki daya.
Ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan tattaunawa da aka gudanar tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Borno ta Kudu.
Askira ya janye wa Sanata Ndume
Sanarwar ta ce jam’iyyar ta yanke hukuncin daukar Sanata Ali Ndume, wanda ke rike da kujerar a halin yanzu, a matsayin dan takara babu hamayya.
Ya ce:
“Ina sanar da ku cikin girmamawa cewa bayan tattaunawa mai fadi, jam’iyyarmu ta APC ta yanke shawarar bai wa Sanata Mohammed Ali Ndume tikitin jam’iyya domin zaben 2027 mai zuwa.”

Source: Facebook
Sanarwar ta kara da cewa bayan wadannan shawarwari, jam’iyyar ta bukaci Askira da ya janye domin bai wa Ndume dama, kuma ya amince da hakan cikin mutunci da biyayya ga jam’iyya.
Askira ya bukaci magoya bayansa a yankin Askira-Uba da dukkanin mazabar Borno ta Kudu da su hada kai tare da mara wa Ndume baya domin cigaban yankin.
Ya ce:
“Kujerar mulki daga Allah take. Idan Allah ya kaddara maka, babu wanda zai iya canzawa; idan kuma bai kaddara maka ba, babu wanda zai iya ba ka.”
Ya kara da cewa:
“Tun da Allah Madaukakin Sarki ya ba su mukaman, ya kamata mu hada kai mu mara masu baya domin cigaban jam’iyyarmu da al’ummarmu.”
An tara wa Sanata Ndume kuɗin fam
A baya, mun wallafa cewa matasan Kudancin Borno sun fara tara miliyoyin Naira domin goyon bayan takarar Sanata Muhammadu Ali Ndume a babban zaben 2027.
Sama da mutane 2,000 daga kananan hukumomi tara sun halarci taron tara kudin tare da bayyana dalilansu na neman Ndume ya koma majalisa don ya wakilce su.
Matasan sun jaddada aniyar tsaya wa kai da fata don sake mara wa Sanata Ali Ndume baya ya ci gaba da wakiltarsu a majalisa saboda wasu halayensa na gari da suka gani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


