Mabiyan Kwankwaso Sun Bullo da Wasu Dabaru da ka Iya Zama Matsala ga Tinubu a Zaben 2027

Mabiyan Kwankwaso Sun Bullo da Wasu Dabaru da ka Iya Zama Matsala ga Tinubu a Zaben 2027

  • Wata kungiyar magoya bayan dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso ta bullo da dabarun dakile sayen kuri'u
  • Kungiyar mai suna KNN ta ce ta kafa tsauraran matakai domin dakile sayen ƙuri'u a jihohi biyar da ke shiyyar Kudu maso Gabas
  • Ta sake jaddada alkawarin samar da kuri'u miliyan biyar ga tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Ƙungiyar Kwankwaso National Network (KNN) ta bayyana cewa ta tanadi dabarun da ta ce ba za su bari a sayi ƙuri'u ko a yi magudin zaɓe ba a jihohin Kudu maso Gabas biyar a zaɓen shekarar 2027.

Ƙungiyar ta kuma ce ta fara tattara mambobinta da sauran tsarinta na ƙasa domin sa ido kan harkokin siyasa kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Kara karanta wannan

Dalilin Najeriya na bude ƙofar tuba ga 'yan bindiga a Najeriya

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa KNN ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da an ƙidaya kowace sahihiyar ƙuri'a.

KNN ta fara wayar da kan masu zaɓe

Mai kula da KNN na shiyyar Kudu maso Gabas, Dakta Ukpai Iro Ukpai, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Umuahia.

A cewarsa, ƙungiyar ta fara gangamin wayar da kan masu zaɓe kan illar sayar da ƙuri'unsu, tana mai bayyana cewa sayen ƙuri'u na daga cikin manyan barazanar da ke hana gudanar da sahihin zaɓe da shugabanci nagari.

Ya ce:

"Mun wayar da kan mambobinmu da magoya bayanmu a faɗin Kudu maso Gabas kan yadda za su ƙi karɓar cin hanci ko amincewa da duk wani yunƙurin sayen ƙuri'unsu."

Ta buƙaci jama'a su guji sayar da makomarsu

Kungiyar KNN ta yi kira ga masu zaɓe da kada su sayar da makomarsu saboda ɗan abin duniya na wucin gadi.

Kara karanta wannan

'Kwankwasiyya ce ta daga Abba': NDC na shirin fattakar gwamnatin Kano a 2027

A cewarta, zaɓin da 'yan Najeriya za su yi a 2027 zai yi tasiri ga makomar ƙasar na tsawon shekaru masu zuwa, saboda haka ya kamata kowa ya gudanar da haƙƙinsa cikin kishin ƙasa.

Ta yabawa haɗakar Obi da Kwankwaso

KNN ta bayyana cewa matasa da dama a Kudu maso Gabas sun sake nuna sha'awar shiga harkokin siyasa bayan haɗakar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Ƙungiyar ta bayyana haɗakar Obi da Kwankwaso a matsayin wani babban ci gaba ga dimokuraɗiyyar Najeriya, tana mai cewa ta sake dawo da fata ga 'yan ƙasar.

KNN ta sake jaddada alƙawarinta na samar da akalla kuri'u miliyan ɗaya daga kowace jiha a yankin Kudu maso Gabas ga tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

An fara tallata Obi/Kwankwaso a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar OKICAN ta jaddada goyon bayanta ga tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a zaben shugaban kasa na 2027.

Kungiyar ta fara aikin tallata tikitin takarar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Arewacin Najeriya.

OKICAN ta ce za ta hada kai da sarakunan gargajiya, kungiyoyin kasuwanni da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kuma karfafa shiga zabe cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262