Kwamishinan Ganduje Ya Amsa Kiran Masoya Tinubu, Zai Nemi Kujerar Sanata a Kano

Kwamishinan Ganduje Ya Amsa Kiran Masoya Tinubu, Zai Nemi Kujerar Sanata a Kano

  • Tsohon kwamishina a zamanin Abdullahi Umar Ganduje a Kano, Garba Yusuf Abubakar ya bayyana aniyar neman takara a karkashin APC a 2027
  • Ya bayyana cewa ba haka kawai ya fito domin bayyana aniyar neman takara ba, illa ya amsa kiran magoya baya da ke ganin zai kawo canji mai ma'ana
  • Garba Yusuf Abubakar ya yi kira ga magoya baya su guji zagi da rikici a harkokin siyasa yayin da 2027 ke kara daukar zafi gabanin babban zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar Kano, Garba Yusuf Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC.

Tsohon kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin taron kaddamar da kudirinsa a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu 2026 inda ya ce kiran masoya ta amsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Garba Yusuf zai nemi kujerar Sanata a Kano
Hon. Garba Yusuf Abubakar tare da magoya baya a Kano Hoto: Hon. Garba Yusuf Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Garba Yusuf Abubakar ya bayyana cewa ya fito ne bayan kira daga kungiyar Tinubu Support Group (TSG), wacce ta bukace shi da ya shiga gasar.

Tsohon kwamishina a Kano zai yi takara

Daily Nigerian ta wallafa cewa a cewar Garba Yusuf Abubakar, ya yi nazari da tuntuba, ya amince da kiran da aka yi masa na tsayawa takara domin bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

Ya kuma bukaci magoya bayansa da su gudanar da siyasa a cikin natsuwa da mutunta juna, ba tare da zagi ko cin mutunci ba.

Garba Yusuf Abubakar, ya ce:

“Zan mara wa duk wanda ya samu tikitin takara baya idan har na sha kaye a zaben fitar da gwani.”

Ya jaddada cewa hadin kai da mutunta juna su ne ginshikin siyasa mai inganci, yana mai cewa burinsa shi ne ganin jam’iyya ta samu nasara gaba daya, ba tare da rarrabuwar kawuna ba.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya yi gargadi kan neman hana kamfen a jihohin Arewa 8

An fara shirin zabe a Kano

Daraktan yakin neman zaben Garba Yusuf Abubakar, Muntari Ishaq Yakasai, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta riga ta fito karara cewa babu batun ba kowa tikitin kai tsaye, yana mai cewa ubangidansa ya shiga takarar ne da cikakken shirin.

Ana shirin fara neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya
Hon. Garba Yusuf Abubakar jim kadan bayan ya ayyana aniyar takara Hoto: Hon. Garba Yusuf Abubakar
Source: Facebook

Ya kuma bukaci magoya baya da su fara aiki tun daga matakin kasa, musamman a matakin unguwanni da kananan hukumomi, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za a kaddamar da kwamitocin yakin neman zabe a hukumance.

Hakazalika, Darakta Janar na cibiyar bunkasa kwazo ta kasa (NPC), Baffa Babba Dan-Agundi, ya bayyana cewa goyon bayan da kungiyar TSG ta bai wa Abubakar ya samo asali ne daga kwarewarsa da kuma gogewarsa a hidimar gwamnati.

Dan-Agundi ya tunatar da cewa Abubakar ya rike mukamin kwamishina a kusan ma’aikatu biyar a lokuta daban-daban, a gwamnatocin jihar Kano na Malam Ibrahim Shekarau da Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Kano: Tsohon kwamishina ya zama shugaban APC

A baya, mun wallafa cewa kwamishinan ma'aikatar ruwa da ya yi murabus a Kano, Umar Haruna Doguwa ya zama sabon shugaban APC ba tare da ya fuskanci wata adawa daga sauran yan jam'iyya ba.

A babban taro da jam'iyyar ta yi, an tabbatar da Doguwa tare da sababbin shugabanni 23 bayan amincewar wakilai 2,420 yayin da ake sake fasalin jam'iyya mai mulkin Najeriya a Kano.

Bayan an kammala zabe, tsohon Shugaban jam'iyya Abdullahi Abbas ya nemi afuwa, ya kuma yi kira ga hadin kai gabanin zaben 2027 domin jam'iyyar ta ci gaba da rike kujerarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng