Zulum Ya Yi abin Mamaki, Ya Nuna Wanda Yake Goyon bayan Ya Gaje Shi a Zaben 2027

Zulum Ya Yi abin Mamaki, Ya Nuna Wanda Yake Goyon bayan Ya Gaje Shi a Zaben 2027

  • Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar, Mustapha Gubio, ya gaje shi a zaɓen 2027
  • Wannan mataki ya fara tada kura a cikin jam'iyyar APC ta jihar, inda masu sharhi ke hango takun-saka tsakanin sansanin Zulum da na Kashim Shettima
  • Hukumar INEC ta riga ta fitar da jadawalin zaɓen 2027, inda za a gudanar da zaɓen gwamnoni a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno – Siyasar jihar Borno ta ɗauki sabon salo yayin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana wanda yake so ya gaje shi a zaben 2027.

Rahoto ya tabbatar da cewa Mustapha Gubio, tsohon kwamishinan ayyuka ne Gwamna Zulum yake so ya dare kujerar gwamna don ci gaba da dora wa a inda ya tsaya.

Kara karanta wannan

Sanata ta fasa kwai, ta fadi yadda aka canja wasu bangarori a sabuwar dokar zabe

Gwamna Babagana Zulum ya ayyana Mustapha Gubio a matsayin wanda yake so ya gaje shi a Borno.
Gwamna Babagana Zulum tare da Mustapha Gubio bayan ya sayi fom din takara a APC. Hoto: Mohammed A. Gubio
Source: Facebook

Gwamna Zulum ya nuna magajinsa

Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa Gubio ne zaɓin gwamnan bayan ya nuna masa fom ɗin takara da ya saya.

"Kwarai, Gubio shi ne d'an takarar da mai girma gwamna yake goya wa baya, kuma sun hadu jim kadan bayan ya sayi fom din tsaya wa takarar a Abuja."

- Malam Dauda Iliya.

Wannan amincewa ta fito fili ne bayan ɓullar wasu hotuna inda aka ga Mustapha Gubio tare da Gwamna Zulum da kuma Sanata Mohammed Tahir Monguno a Abuja.

Borno: Zargin rikici a jam'iyyar APC

Wannan mataki ya nuna cewa Gwamna Zulum ya shirya tsaf domin ganin na hannun damarsa ya karɓi ragamar mulkin jihar muddin wa'adinsa ya ƙare.

Duk da cewa Zulum yana da kyakkyawar alaƙa da magabacinsa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, masu sharhi kan siyasa a Maiduguri sun fara hango alamun sa-in-sa.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya yi hasashen gwamnoni 5 da za su fadi a zaben 2027

Akwai rahotannin da ke nuna cewa Shettima ma yana da nasa d'an takarar da yake son gani ya kai ga gaci, wanda hakan na iya rarraba kan jam'iyyar APC a jihar.

Wani masanin siyasa a garin Maiduguri ya bayyana cewa:

"Akwai alamun samun saɓanin muradu a fili. Zulum da Shettima duka suna da sansanonin da suka fi so, kuma hakan na iya dagula haɗin kan jam'iyya kafin a kai ga zaɓen fidda gwani."
Majiyoyi sun bayyana cewa akwai takun saka a APC bayan Zulum ya nuna wanda yake so ya gaje shi.
Taswirar jihar Borno da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jadawalin zaɓen 2027 daga INEC

A gefe guda kuma, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta fitar da ƙayyadadden lokaci na yadda zaɓukan 2027 za su kasance.

Ga yadda jadawalin yake kamar yadda INEC ta wallafa a shafinta na intanet:

Jadawalin zabe

Ranar gudanarwa

Zaɓen shugaban kasa da majalisar tarayya

16 ga Janairu, 2027

Zaɓen gwamnoni da majalisar jiha

6 ga Fabrairu, 2027

Zaɓen fitar da gwani na jam'iyyu

23 ga Afrilu – 30 ga Mayu, 2026

Fara yakin neman zaben shugaban kasa

19 ga Agusta, 2026

Fara yakin neman zaben gwamna

9 ga Satumba, 2026

Zulum ya yi hawaye a taron siyasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Babagana Zulum, ya zubar da hawaye yayin da yake neman afuwar duk wanda ya bata wa rai a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Gwamnan jihar na Borno ya yi wannan roko ne a wani taron manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Maiduguri a ranar 25 ga watan Afrilu, 2026.

Da yake jawabi, Farfesa Zulum ya jaddada cewa babu wani tikitin takara mafi alheri da ya kamata a mara wa baya kamar na Tinubu da Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com