Tinubu Ya Karyata Jita Jita Ya Jero Ayyukan da Gwamnatinsa ke Yi a Yankin Arewa

Tinubu Ya Karyata Jita Jita Ya Jero Ayyukan da Gwamnatinsa ke Yi a Yankin Arewa

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin cewa an yi watsi da yankin Arewa maso Yamma, ta ce ana gudanar da manyan ayyuka a shiyyar
  • Gwamnati ta bayyana haka ne yayin da ake zargin ta yi watsi da yankin Arewa maso Yamma yayin da aka raya wasu sassan Najeriya
  • Ta bayyana cewa daga cikin manyan ayyukan a yankin akwai aikin layin dogo na Kano–Maradi mai darajar $2bn, wanda aka kai kusan 60% na kammala shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zarge-zargen da ke yawo cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da yankin Arewa maso Yamma.

Gwamnati ta bayyana cewa ba haka kawai ta bar yankin ba, domin ta zuba kudi sosai a fannoni kamar ababen more rayuwa, lafiya da sufuri a yankin.

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwa yau Laraba, NiMet ta hango matsala a Kano da wasu jihohin Arewa

Shugaba Bola Tinubu ya karyata cewa ya watsar da Arewa
Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja kafin fara rangadin nuna ayyukan gwamnati a faɗin ƙasa, wanda zai fara daga Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan aiki a Arewa

Business day ta ruwaito Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da ayyuka na musamman, Tunde Rahman, ya ce an shirya wannan rangadi ne domin gyara fahimtar da wasu ke yi cewa shugaban bai cika alƙawarin da ya ɗauka wa yankin ba.

A cewarsa:

“Mutane da dama na cewa shugaban bai cika alƙawari ga Arewa ba, amma wannan ba gaskiya ba ne. Za ku ga ayyukan da aka fara da kuma waɗanda ake yi a fannonin hanyoyi, kiwon lafiya da kuma layin dogo daga Kano zuwa Maradi.”

Rahman ya ƙara da cewa ana tattara dukkannin nasarorin da gwamnati ta samu domin nuna wa ‘yan Najeriya cewa an samu ci gaba a cikin shekaru uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Da gaske jam'iyyar adawa ta yi wa Kwankwaso, Obi tayin takara? Gaskiya ta fito

Gwamnatin Tinubu na shirin nuna ayyuka a Arewa

Shi ma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce wannan shiri ya samo asali ne daga gibin bayanai da ya sa wasu ke shakkar ayyukan gwamnati.

Shugaba Bola Tinubu ya ce ya yi wa Arewa aiki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

“Idan ba mu faɗi abin da muka yi ba, babu wanda zai faɗa mana. Muna son kafofin watsa labarai su gani da idonsu irin ayyukan da ake yi a ƙasar nan.”

A wajen taron, daraktan sashen sufurin jirgin ƙasa na ma’aikatar sufuri, Finbarr Zirra, ya gabatar da bayanin fasaha kan halin da bangaren layin dogo ke ciki.

Ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na zama cibiyar shirin haɗa layukan dogo na ƙasa baki ɗaya, inda aikin Kano zuwa Maradi mai tsawon kusan kilomita 400 ya zama mafi girma a yankin.

Ya kuma bayyana cewa ana sa ran kammala sashen Kano zuwa Katsina nan da ƙarshen shekara, yayin da ake gina wani reshen daga Kano zuwa Dutse.

Kara karanta wannan

Sanata ta fasa kwai, ta fadi yadda aka canja wasu bangarori a sabuwar dokar zabe

Bola Tinubu zai yi takara a 2027

A baya, kun ji cewa ta tabbata Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake tsayawa takara domin neman wa'adi na biyu a babban zaben shekarar 2027 da ke kara karato wa.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya saya fam din na gani ina so da na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC bayan jam'iyyar ta fitar da jadawalin zaben fitar da gwani.

Haka kuma sayen fam din na zuwa ne yayin da lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kayyade ga jam'iyyu domin fitar da 'yan takara ke kara matsowa don shirya wa 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng