Da Gaske Jam’iyyar Adawa Ta Yi wa Kwankwaso, Obi Tayin Takara? Gaskiya Ta Fito

Da Gaske Jam’iyyar Adawa Ta Yi wa Kwankwaso, Obi Tayin Takara? Gaskiya Ta Fito

  • Jam’iyyar NDC ta fito fili ta yi bayani game da rahotannin da ke cewa ta yi tayin tikitin takarar shugaban ƙasa ga Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
  • NDC ta bayyana haka ne tana mai cewa shafin da aka buga wannan labari ba na ta ba ne, na bogi ne ke yaɗa wannan labari
  • Jagora a jam’iyyar, Seriake Dickson, ya bayyana cewa duk wata sanarwa ta gaskiya sai ta fito ne daga shafukan hukuma da kuma bakin jami’an da aka ba izini kawai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta yi martani mai zafi game da zargin cewa ta yi tayin takara ga wasu manyan yan adawa.

Jam'iyyar ta ta musanta wani rubutu da aka yi wanda aka wallafa bayanai da sunanta cewa ta yi tayin takarar shugaban kasa ga Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Peter Obi ya bayyana dalilin ganawa da Jonathan

NDC ta karyata tayin tikitin takara ga Kwankwaso, Obi
Sanata Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamna, Peter Obi. Hoto: @KwankwasoRM.
Source: Twitter

Kwankwaso, Obi: NDC ta fitar da sanarwa

A cikin wata sanarwa da aka fitar wanda Vanguard ta samu, wanda ya kafa jam’iyyar kuma jagoranta na ƙasa, Seriake Dickson ya sanya wa hannu, ta ce dole ne a ɗauki bayanan da suka fito daga shafukan hukuma kawai a matsayin sahihai.

Rahotanni sun ce jam'iyyar ta shawarci al'umma kan yada jita-jita tana mai roƙon jama’a su riƙa dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma kawai.

Sanarwar ta zo ne bayan yaɗuwar rahotanni daga wani asusun da ba na hukuma ba mai suna @NDCNigNews.

NDC ta yi fatali da ba tikitin takara ga Obi da Kwankwaso
Jagoran jam'iyyar NDC na kasa, Seriake Dickson. Hoto; Sen. Seriake Dickson.
Source: Facebook

Karin haske da jam'iyyar NDC ta yi

Rahoton ya yi ikirarin cewa jam’iyyar na bai wa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso tikitin shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027 da ake tunkara a kasar..

Jam’iyyar ta ce:

“Domin kauce wa shakku, dukkan sanarwar hukuma na jam’iyyar ana fitar da su ne kawai ta shafukanmu da aka tantance da kuma bakin jami’an da aka ba izini.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Peter Obi sun samu tayin tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027

NDC ta bayyana shafukanta na sadarwa a Najeriya

NDC ta kuma jero shafukan sada zumunta na hukuma da take amfani da su da sunan @nigeriandchq a X, Facebook, Instagram da TikTok, tare da gidan yanar gizon ta, cewar TheCable.

Jam’iyyar ta buƙaci jama’a, kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki su yi watsi da duk wani bayani daga asusun da ba na hukuma ba, tare da tabbatar da sahihancin labarai ta hanyoyin da aka amince da su.

Jam'iyyar NDC ta caccaki Kalu saboda yabon Tinubu

Mun ba ku labari a baya cewa jam’iyyar NDC ta yi wa Sanata Orji Uzor Kalu rubdugu kan yabon da ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu game da halin tattali arziki.

A bayanin da ya yi, Kalu ya nuna cewa shugaba Tinubu ya yi ayyuka masu kyau a Najeriya kuma hakan zai saka 'yan kasa su zabe shi domin sake ba shi dama a karo na biyu.

Sai dai NDC ta masa kakkausan martani, inda ta ce maganganun Sanatan ba daidai ba ne domin a cewarta 'yan Najeriya na shan wahala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.