Kai Mutane Hajji, Taimakon Almajirai da Ayyukan Peter Obi a Arewa
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya musanta zargin nuna wariya ga 'yan Arewa yayin da yake gwamnan Anambra
- Obi ya ce ya riƙa ɗaukar nauyin Musulmai zuwa aikin Hajji da Kiristoci zuwa ziyara, sannan yana tallafa wa makarantun Almajirai
- Tsohon gwamnan ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, zai haɗa kan Najeriya ba tare da nuna bambancin addini ko yanki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya yi martani kan zargin da ake yi masa na nuna wariya ga 'yan Arewa lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.
Peter Obi ya yi magana ta musamman game da hada kan 'yan Najeriya idan Allah ya ba shi nasara a zaben shugaban kasar 2027.

Source: Facebook
Channels Television ta rahoto cewa Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics, inda ya ce aikinsa a lokacin mulkinsa ya nuna cewa bai taɓa bambance mutane bisa addini ko yanki ba.
Obi ya nuna kula ga Arewa
Peter Obi ya ce mai ba shi tsaro (ADC) a lokacin yana daga jihar Kaduna kuma Musulmi ne, yana mai cewa hakan ya nuna yadda yake bai wa kowa dama ba tare da la'akari da addini ko asalinsa ba.
Ya ƙara da cewa a lokacin da yake gwamna, yana ɗaukar nauyin Kiristoci zuwa ziyara da kuma Musulman jihar Anambra zuwa aikin Hajji a Saudiyya.
A cewarsa:
"ADC na daga Kaduna ne kuma Musulmi ne. A lokacin da nake gwamna, ina ɗaukar nauyin Kiristoci zuwa ziyara, haka kuma ina ɗaukar nauyin Musulmai zuwa aikin Hajji. Har yanzu ina tallafa wa makarantun Almajirai guda huɗu."
Obi ya bayyana cewa ya toni rijiyoyin ruwa a Arewa tare da tallawa makarantu da dama a yankin domin habaka ilimi da rayuwar mutane.
Batun hada kan Najeriya
Obi ya ce ba gaskiya ba ne zargin cewa ya taɓa yin kalaman da ke nuna ƙyamar 'yan Arewa ko kuma zai raba kan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa a tsawon shekarun da ya yi yana siyasa, ya kai ziyarar jaje da taimako zuwa jihohin Arewa da dama, musamman waɗanda rikicin Boko Haram ko bala'o'i suka shafa.
Ya tuna yadda ya je jihar Borno domin yi wa tsohon gwamna Ali Modu Sheriff ta'aziyyar rasuwar ɗan'uwansa a farkon rikicin Boko Haram, lokacin da mutane da dama ke tsoron zuwa yankin.

Source: Facebook
Obi ya kuma ce masu dafa masa abinci a tsawon shekaru takwas da ya yi yana gwamnan Anambra duk 'yan Arewa ne.
Ga bidiyon da Obi ya yi magana da Imran Muhammad ya wallafa a X:
Obi ya caccaki Bola Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Peter Obi ya soki salon sadarwar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana mai cewa ya kamata shugaban ƙasar ya riƙa yin jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya.
Obi ya ce bai dace shugaban ƙasa ya dogara ga masu taimaka masa wajen bayyana manufofin gwamnatinsa ba, yana mai cewa 'yan Najeriya suna son jin bayani kai tsaye daga bakinsa.
Ya buƙaci Bola Tinubu ya fito ya tattauna da jama'a kan halin da ƙasar ke ciki da kuma matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo gyara.
Asali: Legit.ng


