Ba Tazarce: Yadda aka Shirya Juyawa Tinubu Baya a Jihohin Yarabawa a 2027

Ba Tazarce: Yadda aka Shirya Juyawa Tinubu Baya a Jihohin Yarabawa a 2027

  • An kaddamar da shugabannin jam'iyyar adawa ta ADC a Kudu maso Yammacin Najeriya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ta shirya kifar da Bola Tinubu da sauran 'yan APC a jihohin da suke yankin gaba daya a zaben 2027 mai zuwa
  • ADC ta bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ta yi a yankin, inda ta bayyana cewa Tinubu bai kawo wani cigaba ba a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Jam’iyyar ADC a yankin Kudu maso Yamma ta bayyana shirinta na kayar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a yankin, tana mai cewa ‘yan Najeriya sun shirya fatattakar shi.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Bola Tinubu ya saye fom din takara a karkashin APC domin neman tazarce a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya amsa kiran masoya Tinubu, zai nemi kujerar sanata a Kano

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tribune ta rahoto cewa ADC ta sanar da shirin kawar da Tinubu ne a taron manema labarai na farko na yankin Kudu maso Yamma karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa Hon. Akinbowale Omole.

An nada shugabannin ADC

Yayi bikin kaddamar da shugabannin jam'iyya, Akinbowale Omole ya ce jam’iyyar ADC ta shiga wani sabon mataki na farfadowa da kuma tattara magoya baya

A cewarsa, an nada da shugabannin yankin a hukumance a Ibadan bayan amincewar kwamitin koli na jam’iyyar da kuma kwamitin zartarwa na kasa.

Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda yanzu shi ne sakataren jam’iyyar na kasa, shi ne ya jagoranci bikin kaddamarwar.

ADC za ta kifar da Tinubu

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa ADC ta zama mafi ingancin sauyi da za a samu ga abin da ya kira gazawar gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ya kara da cewa jam’iyyar na da kudurin ceto Najeriya daga wahalhalu, rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da kuma shugabanci mara kyau.

Kara karanta wannan

2027: An kunna rikici a PRP da ke shirin kawar da Tinubu, ADC ta magantu

Dangane da yanayin siyasar yankin Kudu maso Yamma, Omole ya ce bai kamata goyon bayan shugaban kasa ya ta’allaka kan yankin mutum ba, sai dai kan auna aikin da ya yi, gaskiya da kuma ci gaban tattalin arziki.

Ya kuma ce al’ummar Yarabawa sun shahara a duniya da dabi’ar da ta kunshi rikon amana da shugabanci mai tsari, yana mai cewa gwamnatin yanzu ba ta wakiltar wadannan dabi’u.

Shugaba Bola Tinubu da Bolaji Abdullahi
Shugaba Bola Tinubu a hagu da kakakin ADC Bolaji Abdullahi a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Shafin ADC Vanguard ya wallafa hotunan taron jam'iyyar da yadda ta bude babban ofishinta a Kudu Maso Yamma a kafar X.

Shugabannin ADC da aka nada

Daga cikin sababbin shugabannin jihohi da aka gabatar a wajen taron sun hada da:

Jimoh Afees Adelowo – Jihar Oyo

Azeez Issa Adesiji – Jihar Osun

George Ashiru – Jihar Legas

Emmanuel Famojuro – Jihar Ogun

Bamidele Ekunola – Jihar Ekiti

Tola Alabere – Jihar Ondo

ADC: "APC ta jefa rikici a PRP"

A wani labarin, kun ji cewa kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya zargi jam'iyyar APC da jefa rikici a jam'iyyar adawa ta PRP.

Ya bayyana haka ne bayan wani bangare ya bulla a PRP kwanaki kadan bayan zaben shugabanni a babban taron da ta yi a Abuja.

Sai dai shugaban jam'iyyar, Dr Hakeem Baba Ahmed ya ce shi ne halastaccen jagoran PRP a Najeriya kuma babu mai ja da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng