Kano: Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya ba da Mamaki, Ya Raba wa Mata Tallafin 'Omo'
- Shugaban karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano bayan an hango shi yana raba wa mata tallafin da ƴan siyasa ke ba mutanensu
- Sai dai yayin da wasu ke raba kuɗi ko dabbobin kiwo, Hon. Abdullahi Sa'idu ya ga dacewar ya raba sinadarin wanke-wanke da ake kira 'omo'
- An tara mata akalla 500, sun hau kan layi yayin da kowacce ke karban abin wanke-wanke da wanki tana wuce wa domin ta bayanta ta samu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban ƙaramar hukumar Kiru a jihar Kano, Abdullahi Saidu, ya raba kayan wanke-wanke ga mata 500 a mazabarsa a wani shiri da aka bayyana a matsayin tallafi ga rayuwar yau da kullum.
An ce rabon ya shafi mata daga unguwar Yalwa cikin Kiru ƙaramar hukumar Kiru inda aka ba su nau’o’in sabulu irin su Omo, Klin da kuma Viva.

Kara karanta wannan
Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito a cewar shugaban, an tsara wannan shiri ne domin tallafa wa mata da kuma rage masu wasu nauyin ayyukan gida.
An raba wa mata sabulu a Kano
Hon. Abdullahi Saidu ya bayyana cewa irin waɗannan matakai na taimaka wa mata wajen sauƙaƙa rayuwa, musamman a cikin al’ummomin karkara.
Sai dai wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ganin ƙara motsin siyasa kafin zaɓuɓɓuka masu zuwa, inda masu sa ido ke lura da yadda ake ƙara gudanar da irin waɗannan shirye-shiryen kai-tsaye ga mata da marasa galihu.
Haka kuma, a wani makamancin mataki, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya raba pampers ga mata masu juna biyu a wasu sassan mazabar.

Source: Facebook
Mazauna yankin sun bayyana cewa duk da cewa irin waɗannan tallafi suna ba da ɗan sauƙi na wucin gadi, amma suna nuna yadda harkokin siyasa ke fara bayyana a matakin al’umma tun kafin lokaci ya yi nisa.

Kara karanta wannan
Ganduje ya faɗi abin da ya kori Gawuna daga APC, ya taɓo batun butulci a siyasar Kano
Jama'a sun yi mamakin rabon sabulu a Kano
Wannan rabon sabulu ya ja hankalin jama'a da jama'a, musamman ganin cewa ana yi ne dan da fara gangamin neman zaben 2027.
Wani matashi, Muhammad Aliyu Junaid ya ce:
“Ya kamata wani ya gaya wa shugaban cewa tsofaffi ba su bukatar sabulu don wanke kaya… Mtseww!”
Shi ma Auwal Nasir Abdullahi bayyana cewa:
"Siyasa a Arewacin Najeriya ta cika da abubuwan kunya. Wace irin ƙima sabulu ke da ita? Allah ya ba mu shugabanni masu tsoronSa da za su nuna tausayi.”
Fatihu Saeed ya ce:
“Shugaba gaba ɗaya yana nuna kansa saboda ya raba sabulu da bai wuce N1700 ba. Ana ɗaukar hotunan mata. Wannan abin kunya ne.”
Gwamnan Kano ya magantu kan rashin tsaro
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya zargi wasu yan siyasa da amfani da matsalar tsaron Najeriya domin cimma burinsu.
Gwamna Abba Gida-Gida ya ce wasu mutane marasa kishin kasa ke rura matsalar tsaro, wanda hakan ke kawo cikas ga kokarin samar da tsaro a kasar nan.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tsare rayukan al'umma a fadin jihar Kano da ke fama da matsalolin tsaro kamar fadan daba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
