Mutanen Jihar Kano na cikin Alheri a Mulkin Tinubu, An Raba 2a Talakawa Naira Biliyan 48

Mutanen Jihar Kano na cikin Alheri a Mulkin Tinubu, An Raba 2a Talakawa Naira Biliyan 48

  • Gwamnatin tarayya ra rabawa talakawa da masu karamin karfi tallafin Naira biliyan 48 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano
  • Ministan harkokin jin kai da yakar talauci, Dakta Bernard Doro ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai Kano domin duba yadda shirin ke aiki
  • Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar wannan shiri da su yi amfani da kudin da aka ba su wajen inganta sana'o'insu don zama masu dogaro da kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta raba sama da Naira biliyan 48 ga magidanta masu rauni da talakawa a jihar Kano karkashin shirin tallafin kuɗi na HoPE-CT.

Ministan harkokin jin kai da rage talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar ganawa da masu cin gajiyar shirin a makarantar firamare ta Unguwa Uku da ke karamar hukumar Tarauni.

Kara karanta wannan

Kano ta bar jihohi a baya, ta cika sharadin inganta ilimi a Najeriya

Bernard Doro.
Ministan Harkokin Jin Kai, Dr. Bernard Doro lokacin da ya kawo ziyara jihar Kano Hoto: Dr. Bernard Doro
Source: Facebook

Hakan na kunshe a wata sanarwa da Dakta Doro ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Talata, 28 ga watan Afrilu, 2026.

Yadda aka raba fiye da N48bn a Kano

Ya ce an aiwatar da shirin a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, inda aka raba jimillar N48,130,875,000 a kashi uku, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa an raba Naira biliyan 19.6 a kashi na farko, N14.5bn a kashi na biyu, sannan N13.9bn a kashi na uku, inda kowane mai cin gajiyar shirin ya samu N75,000.

Abin da ya sa Ministan jin-kai ya je Kano

Doro ya ce ya kai ziyara jihar Kano ne ba don komai ba dai domin duba tasirin da shirin tallafin kudin ya yi kai tsaye tare da sauraron masu amfana da shi.

“Na zo ne domin ganin yadda shirin ke aiki a kasa, da sauraron masu cin gajiya domin tabbatar da cewa manufofin gwamnati na haifar da sakamako mai kyau,” in ji shi

Kara karanta wannan

An kunyata 'yan jarida a zaman shari'ar wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki a Najeriya

Ministan ya bayyana cewa shirin yana cikin wani babban tsari mai taken “One Humanitarian, One Poverty Response System”, wanda ke da nufin tabbatar da gaskiya da hadin kai wajen aiwatar da shirye-shiryen rage talauci.

Taron Kano.
Mata masu cin gajiyar tallafin gwamnatin tarayya a taron da aka shirya a makarantar firamare ta Unguwa Uku da ke karamar hukumar Tarauni, Kano Hoto: Dr. Bernard Doro
Source: Facebook

Gwamnati ta fara gyara shirin

Ya kara da cewa ana sake fasalin shirin domin ya zama hanyar da za ta taimaka wa masu cin gajiyar su fita daga dogaro da tallafin kudin zuwa masu cin gashin kai.

Dakta Doro ya gargadi jama’a cewa shirin kyauta ne, yana mai kira gare su da su kai rahoton duk wani cin zarafi ko karbar kudi da wasu ke yi domin sanya su a shirin.

Ya kuma bukace su da su yi amfani da kudaden yadda ya kamata ta hanyar zuba jari a sana’o’in da za su inganta rayuwarsu.

Gwamnatin Tinubu za ta ba manoma bashi

A baya, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta shirya rabawa manoma Dala miliyan 500 domin inganta harkokin noma a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar hada-hadar kudin hadin gwiwa ta kasa, Emmanuel Atamand ya yi wa manoma wannan albishir na samun rancen kudi daga gwamnatin Tinubu.

Atama ya tabbatar da cewa bashin dala miliyan 500 da Najeriya za ta karbi daga bankin duniya zai kai ga manoma na gaskiya a Najeriya cikin sauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262