Kananan hukumomin Najeriya
Ɗan Ministan Ayyuka David Umahi mai shekaru 28, Osborn Umahi, ya lashe kujerar shugaban Ohaozara, inda ya yi alkawarin yin aiki ba tare da albashi ba.
APM ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 a Bauchi, tare da samun kujerun kansiloli 319 cikin 323 a zaben kananan hukumomin jihar.
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya kira jam’iyyun adawa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi matsorata, bayan APM ta lashe kujerun shugabanni 20.
A labarin nan za a ji cewa rundunar yan sandan kasar nan reshen jihar Bauchi ta sanar da jama'a shirye-shiryen da ake yi game da zaben kananan hukumomi.
Mataimakin Gwamnan Katsina Faruk Jobe ya ce kananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar na fuskantar hare-hare a 2023, amma tsaro ya inganta sosai tun daga lokacin.
Majalisar dokokin Kano ta ce tana binciken zarge-zargen almundahana da rashin iya mulki kan shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar ranar Talata.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin kananan hukumomin Bebeji, Rogo da Bagwai daga bakin aikinsu na tsawon watanni uku don gudanar da bincike.
Shugaban ƙaramar hukumar Kuje ya naɗa Ibrahim Danladi mataimaki na musamman, yana mai cewa mukamin nishaɗi ne, ba na rawa kamar yadda aka ruwaito ba.
A labarin nan, za a ji cewa Kwamared Abdullahi Ghali Basaf, tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kano ya koma sana'ar dinki bayan ya rasa kujera.
Kananan hukumomin Najeriya
Samu kari