"Abba ne Jagora a Kano": Ganduje Ya Yi Magana kan Naɗa Garo Mataimakin Gwamna
- Tsohon gwamnan, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf bai yi kuskure ba da ya kira kansa jagoran APC a Kano ba
- Ganduje, wanda tsohon shugaban APC ne na kasa ya ce shi da kansa ya taba daga hannun gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin jagora
- Ya bayyana nadin da Abba ya yi wa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna da ɗora ƙwarya a gurbinta saboda wasu dalilai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bai yi kuskure ba da ya kira kansa jagoran jam’iyyar APC a Kano.
A kwanakin baya ne gwamnan ya fito ya bayyana cewa ba ya karɓar umarni daga hannun kowa, har da tsohon shugaban APC, Ganduje a Kano, domin shi ne jagoran jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Source: Facebook
A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, Ganduje ya bayyana cewa shi da kansa ya taba daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da bayyana shi a matsayin jagora a Kano.
Ganduje ya yi bayani kan nadin Garo
A cikin tattaunawar, Ganduje ya bayyana cewa nadin mataimakin gwamna abu ne da ke karkashin ikon gwamna, yana mai cewa Allah ne Ya ba shi, kuma gwamna ne ya ba shi.
Ya ce:
"Mu ƴan kallo ne, mu ƴan bada shawara ne. Amma abin da zan gaya muku shi ne, ba shi wannan mukami na mataimakin gwamnan jihar Kano, an ajiye kwarya a gurbinta."
Ya kara da cewa Murtala Sule Garo ya rike mukamai daban-daban a baya, wanda hakan ya nuna gogewarsa a harkokin mulki.
"Murtala Sule Garo ya yi shugaban karamar hukuma har sau 2, kuma ya yi shugaban kungiyoyin ciyamomin ƙananan hukumomi, ya yi Kwamishina na ƙananan hukumomi shekara takwas."
Ganduje ya bayyana cewa mukamin mataimakin gwamna mukami ne da ke bukatar mutum mai hakuri da tunani, wanda zai iya taimakawa gwamna wajen tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata.
Ganduje ya taya Garo murna
Tsohon gwamnan ya kara da cewa Murtala Sule Garo mutum ne mai hakuri, wanda hakan ne ya sa ake yi masa murna kan wannan matsayi da aka ba shi domin ya fi duka masu neman kujerar cancanta.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa bisa tsarin ladabi na jam’iyyar APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne shugaban APC a Kano.
Ya ce hakan ya sa ya shige masa gaba domin ya zamana shi kadai ne zai yi wa jam’iyyar takarar gwamna a zaben 2027.
Ganduje ya jaddada cewa duk da kasancewarsa tsohon gwamna, rawarsa a yanzu ita ce ta bada shawara kawai, ba ya yin katsalandan a harkokin mulki.
Sakon Ganduje ga Kwankwaso'
A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Malam Ibrahim Shekarau bayan rasuwar yayansa.
Ganduje ya yi magana game da Rabiu Kwankwaso da ake kiransa makiyinsa, a nan ya ce yana daukarsa a matsayin dan uwa a addini Duk da sabani da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan
Ganduje ya yi karatun ta natsu, ya gano dalilin da ya sa ake yawan samun mabarata a Arewa
Tsohon shugaban APC na ƙasa ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ayyukan ci gaba a Kano tare da masa addu’ar samun nasara a al'amuransa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
