Ganduje Ya Faɗi Abin da Ya Kori Gawuna daga APC, Ya Taɓo Batun Butulci a Siyasar Kano

Ganduje Ya Faɗi Abin da Ya Kori Gawuna daga APC, Ya Taɓo Batun Butulci a Siyasar Kano

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa aka gan shi da shugaban ƙasa a kwanakin baya
  • Ganduje ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kira shi domin tattauna rikicin siyasar Kano da ta dauki zafi
  • Tsohon gwamnan ya kuma yi magana game da sauya shekar tsohon mataimakin, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da tasirin hakan a siyasar Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi bayani kan abin da ya tattauna da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan wata muhimmiyar gana wa a baya.

Ganduje ya ce a lokacin da Tinubu ya kira shi, siyasar Kano ta shiga bakin jama'a musamman saboda sauya sheƙar tsohon ɗan takarar jam'iyyar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan

"Abba ne jagora a Kano": Ganduje ya yi magana kan naɗa Garo mataimakin gwamna

Ganduje ya ce Tinubu ya kira shi don tattauna siyasar Kano
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da Abdullahi Ganduje. Hoto: @GovUmarGandujee
Source: Twitter

A wata hira da BBC Hausa, Ganduje ya ce shugaban kasa ne da kansa ya kira shi domin jin halin da ake ciki a Kano, musamman bayan sauya shekar , Dr. Gawuna zuwa jam’iyyar ADC.

Ganduje ya magantu kan zama da Tinubu

A hirar, Ganduje ya bayyana cewa a lokacin da aka yi wannan ganawa, siyasar Kano ta shiga wani yanayi na rikicewa, lamarin da ya jawo hankalin shugaban kasa.

A cewarsa, Tinubu ya nuna damuwa kan yadda al’amuran siyasa ke tafiya a jihar, wanda hakan ya sa ya gayyace shi domin tattaunawa domin ya san halin da ake ciki.

Ya ce:

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ya gayyace ni, yana so ya ganni saboda siyasar Kano ta rikice.”

Gawuna bai ci amana ba – Ganduje

Dangane da sauya shekar da Nasiru Yusuf Gawuna ya yi zuwa jam'iyyar ADC, Ganduje ya bayyana cewa bai dauki hakan a matsayin cin amana ko butulci ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi karatun ta natsu, ya gano dalilin da ya sa ake yawan samun mabarata a Arewa

A cewarsa, sauya jam’iyya wani bangare ne na dimokuraɗiyya, inda kowane ɗan siyasa ke da ‘yancin bin ra’ayinsa da abin da ya ga ya dace da makomarsa.

Ganduje ya ce kila Gawuna ya bar APC ne saboda Abba
Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna Hoto: @AbubakarmusaDK1, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Ya ce:

“Bai min laifi ba, bai min butulci ba, domin dimokuraɗiyyar zamani ra’ayi ne.”

Ya kara da cewa akwai yiwuwar Gawuna ya yanke shawarar sauya jam’iyya ne bisa nazari da hangen nesan siyasa, amma ba don ya samu matsala da kowa a APC ba.

A cewar Ganduje:

“Watakila ya ga gwamna ya shigo, saboda haka babu takarar gwamna ke nan. Tun da da gwamna ya shigo, mun ce zai tafi falle na biyu."

Ganduje ya jaddada cewa, ko da yake ba shi da tabbacin dalilin sauya shekar Gawuna, amma yana ganin hakan na iya zama wata hanya ce da ya zaba domin neman ci gaba da tasiri a harkokin siyasa.

Ganduje ya yabi gwamnan Kano

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ya nada Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Ya bayyana cewa tsakaninsa da Abba shawara ce kawai ba umarni ba, kuma tsari da ladabin jam'iyyar APC ya bayyana cewa duk gwamna a jiharsa shi ne jagoran jam'iyya.

Ganduje ya kara da cewa Murtala Sule Garo shi ne ya fi kowa cancanta daga cikin waɗanda suka so a ba su kujerar mataimakin gwamnan Kano saboda nagartarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng