Lauyoyi Sun Gano Matsalar da za Ta Kawo Cikas ga Tinubu a 2027
- INEC ta wallafa takardun takarar Bola Tinubu na zaben 2027, amma babu bayanan makarantar firamare da sakandare a cikin takardun da aka fitar
- Jam'iyyun ADC da NDC tare da wasu manyan lauyoyi sun ce rashin wadannan bayanai ya sake tayar da muhawarar da aka yi kan takardun karatun shugaban kasa
- Sai dai INEC ta bayyana cewa ba aikinta ba ne tantance sahihancin takardun karatun 'yan takara kafin wallafa su domin jama'a su duba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sabuwar muhawara ta sake kunno kai kan takardun karatun shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta wallafa takardun 'yan takarar shugaban kasa na zaben 2027.
A cikin takardun da INEC ta wallafa, an nuna cewa Tinubu ya gabatar da shaidar digirinsa daga Jami'ar Chicago da kuma takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC), amma babu bayanan takardun firamare da sakandare.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na tsaka mai wuya, jam'iyyar PDP ta yi bayani

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa wannan mataki ya sake tayar da muhawarar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa na 2023 kan takardun karatun shugaban kasar.
Bayanin da INEC ta yi
INEC ta bayyana cewa ba ta da alhakin tantance sahihancin takardun karatu ko sauran bayanan da 'yan takara ke gabatarwa kafin wallafa su.
Hukumar ta ce aikin tantancewa ba ya cikin nauyin da doka ta daura mata, illa dai wallafa bayanan domin jama'a su duba.
Abin da lauyoyi suka fada
Babban lauya mai mukamin SAN, Mumini Jimoh, ya ce doka ta tanadi cewa dole ne mai neman takarar shugaban kasa ya mallaki akalla takardar shaidar kammala sakandare.
Ya ce idan har babu irin wannan takarda, hakan na iya haifar da matsalar shari'a, amma yana ganin watakila kuskuren shigar da bayanai ne, ba wai shugaban kasa bai cika sharadin ba.
Shi ma wani SAN, Mohammed Abeni, ya ce rashin bayyana takardun firamare da sakandare ya bar gibi da ka iya haifar da shakku, musamman ganin takaddamar da aka dade ana yi kan bayanan karatun shugaban kasa.
Maganar ADC, Atiku da NDC
Jam'iyyar ADC ta zargi shugaban kasa da kokarin boye wani abu ta hanyar kin bayyana takardun firamare da sakandare a takardun da aka mika wa INEC.
Mai magana da yawun jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce hakan ya kara karfafa rade-radin da ake yi cewa akwai abubuwan da ba a bayyana ba game da tarihin karatun shugaban kasa.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce idan rahotannin da aka fitar gaskiya ne, to batun ba kuskuren gudanarwa ba ne, illa yana da alaka da gaskiya da amincin bayanan da shugabanni ke gabatarwa.

Source: Facebook
The Sun ta rahoto cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bukaci shugaban kasa ya fito ya yi wa 'yan Najeriya cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka bar gurbin bayanan firamare da sakandare a takardunsa.
PDP ta yi farin ciki da matakin INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa bangaren jam'iyyar PDP mai biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi maraba da wallafa sunan Sanata Sandy Onor a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.
Jam'iyyar ta ce matakin INEC ya kawo karshen rade-radin cewa PDP ba za ta iya fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.
PDP ta kuma yaba wa INEC, bangaren shari'a da hukumomin tsaro, tana mai cewa matakin ya kara tabbatar da cewa jam'iyyar na cikin shirin fafatawa a babban zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

