Lokuta 6 da Ibrahim Shekarau Ya Taba Sauya Jam'iyyun Siyasa a Najeriya

Lokuta 6 da Ibrahim Shekarau Ya Taba Sauya Jam'iyyun Siyasa a Najeriya

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya raba gari da jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Sanata Ibrahim Shekarau ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Afirilun 2026.

Sanata Ibrahim Shekarau ya koma APC bayan barin PDP
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau Hoto: Malam Ibrahim Shekarau
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro lokutan da tsohon gwannan na Kano kuma tsohon Ministan ilmi ya taba sauya jam'iyyun siyasa.

Shekarau ya kafa tarihi a Kano

Malam Shekarau ya kasance mamba a rusasshiyar jam'iyyar ANPP, wadda a karkashinta ya yi gwamnan Kano.

A shekarar 2003, Malam Shekarau ya ya kayar da gwamna mai ci, inda ya doke Rabiu Musa Kwankwaso kuma ya zama na farko da ya zarce a ofis.

Bayan wannan gagarumar nasara, an sake zaben Malam Shekarau a shekarar 2007, don haka ya yi wa'adi biyu a jere a ofis.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamnan jihar Kano, Shekarau ya fice daga jam'iyyar PDP

Jam'iyyun da Shekarau ya sauya sheka

Yadda Malam Shekarau ke sauya sheka yawanci yana faruwa ne sakamakon gwagwarmayar neman iko a siyasar Kano, musamman dadaddiyar takun-sakarsa da Rabiu Musa Kwankwaso.

Ga jerin lokutan da Shekarau ya taba sauya sheka:

1. ANPP zuwa APC

Shekarau ya rabu da jam'iyyar ANPP wadda ya yi wa'adin gwamna sau biyu a karkashinta shekarar 2013.

Shekarau ya bar ANPP zuwa jam'iyyar APC wadda jam'iyyun adawa suka ruguje zuwa cikinta domin tunkarar zaben shekarar 2015.

2. APC zuwa PDP

A shekarar 2014, Malam Shekarau ya koma PDP bayan raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta APC, rahoton jaridar Premium Times ya nuna hakan.

Sauya shekar Shekarau daga APC zuwa PDP a wancan lokacin na da nasaba da shigowar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar.

Ganin cewa an mika tsarin jam'iyyar a Kano ga Rabiu Musa Kwankwaso, Malam Shekarau ya nemi mafaka a PDP har yzama ministan ilmi.

3. PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya soke batun komawa jam'iyyar APC, an ji dalili

Bayan shan kashin da PDP ta yi a babban zaben 2015, Malam Shekarau ya ci gaba da zama a jam’iyyar na tsawon shekaru kafin ya sake komawa APC a watan Satumban 2018.

A wani yanayi na ba-zata, Rabiu Musa Kwankwaso shi ma a daidai lokacin ya fice daga APC ya koma PDP.

Ba a dade ba tarihi ya sake maimaita kansa. Malam Shekarau ya ji cewa shugabancin PDP na kasa yana nuna fifiko ga kungiyar “Kwankwasiyya” ta Kwankwaso a Kano.

Domin gudun kada a mayar da shi saniyar ware, Malam Shekarau ya koma APC, inda daga baya ya lashe kujerar sanatan Kano ta Tsakiya a shekarar 2019, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

4. APC zuwa NNPP

Gabanin zaben 2023, sabanin cikin gida ya tsananta tsakanin Malam Shekarau da Gwamna Abdullahi Ganduje na lokacin.

Malam Shekarau ya ji cewa Ganduje ya tauye shi sakamakon cikakken ikon da yake da shi a kan jam’iyyar tun daga tushe.

Sakamakon haka, ya koma jam’iyyar NNPP, wadda Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta a lokacin, jaridar The Nation ta kawo rahoto kan hakan.

Na dan kankanin lokaci, ya birne takun-sakarsa da babban abokin hamayyarsa, Kwankwaso, inda suka hada karfi da karfe domin yaki da Ganduje, suna neman dandalin da zai tabbatar wa mabiyansa samun takarar zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda APC ke fatan samun miliyoyin kuri'u a Kano da Katsina a zaben 2027

Shekarau ya sauya sheka zuwa APC
Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano Hoto: Malam Ibrahim Shekarau
Source: Facebook

5. NNPP zuwa PDP

Zaman Malam Shekarau a jam'iyyar NNPP ya kwashe watanni uku kacal inda ya fice zuwa PDP, jaridar The Punch ta kawo labarin sauya shekar.

Ya koma PDP a watan Agustan 2022, yana zargin cewa Kwankwaso da shugabancin NNPP sun gaza cika yarjejeniyar saka magoya bayansa a cikin jerin ‘yan takarar jam’iyyar na zaben 2023.

Shekarau ya koma da dukkan rundunarsa ta siyasa zuwa PDP domin marawa takarar shugaban kasa ta Atiku Abubakar baya a 2023.

6. PDP zuwa APC

A ranar Lahadi, 19 ga watan Afirilun 2026, Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Shekarau ya sanar da komawarsa zuwa APC bayan barin PDP mai adawa a jihar.

Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga PDP ne tare da Sanata Bello Hayatu Gwarzo da sauran magoya bayansa a siyasa.

Kara karanta wannan

Amurka ta cafke wasu ƴan Najeriya 8 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci? Gaskiya ta fito

Gwamna Bala ya fasa komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fasa komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Gwamna Bala ya fasa komawa APC ne bayan jam'iyyar ta ki amincewa da tsarin rabo na 60-40 da zai ba shi ikon zama jagoranta a jihar.

Sakamakon haka, gwamnan da magoya bayansa sun bayyana cewa a shirye suke su tattauna da sauran jam’iyyun siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng