Amurka Ta Cafke Wasu Ƴan Najeriya 8 da Ke Ɗaukar Nauyin Ta'addanci? Gaskiya Ta Fito

Amurka Ta Cafke Wasu Ƴan Najeriya 8 da Ke Ɗaukar Nauyin Ta'addanci? Gaskiya Ta Fito

Abuja - A 2023, wani rahoto ya nuna yadda matsalar tsaro ta zama daya daga cikin manyan matsaloli 10 da Najeriya take fuskanta, da ya cancanci a magance su cikin gaggawa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rahoton ya nuna cewa, duk da cewa gwmanati na shimfida manyana ayyukan raya kasa, sai dai, sukan zamo marasa armashi a duk lokacin da rayukan 'yan kasar ke cikin tashin hankali.

An gano gaskiya da aka yada rahoton cewa sojojin Amurka sun kama 'yan Najeriya 8 kan daukar nauyin ta'addanci.
Kanal Patrick Doyle (tsakiya) yana jawabi a taron mika motocin yaki 24 da Amurka ta ba sojojin Najeriya a filin motsa jiki na Birged ta 9. Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Ikirarin sojojin Amurka sun kama 'yan Najeriya 8

A yayin da 'yan Najeriya ke kwadayin jin labari mai daɗi game da kama waɗanda ke rura wutar ta’addanci, wani ma'abocin Facebook, Manny Soft, ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun kama mutane takwas da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Manny Soft, ya wallafa bidiyon da ya yi bayani game da lamarin, inda aka ji yana cewa:

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

"Sojojin Amurka sun kama 'yan Najeriya takwas da ke daukar nauyin ta'addanci a kasar nan. Idan kuna son sanin ko su wane ne, ku bibiyi wannan shafi, kuma ku tura bidiyon ga abokanku."

Ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, 2026, Legit Hausa ta fahimci cewa bidiyon ya samu masu kallo fiye da 8,000, sannan mutane 81 sun yi magana a kai, mutane 139 sun tura bidiyon ga mabiyansu.

Legit Hausa ta fahimci cewa Manny Soft ya dade yana wallafa ire-iren wadannan bidiyo, amma yana sauya adadin da yake cewa an kama, daga takwas zuwa 12, zuwa 15.

Bincike kan ikirarin kama 'yan Najeriya 8

Kafar binciken kwakwaf ta Dubawa ta gudanar da bincike domin gano gaskiya game da ikirarin cewa sojojin Amurka sun kama 'yan Najeriya takwas da ke daukar nauyin ta'addanci.

Wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa a watan Fabrairu 2026, ya nuna cewa gwamnatin Amurka, karkashin ofishin kudi na hukumar OFAC, ta sanya takunkumi kan 'yan Najeriya takwas kan zargin alaka da kungiyoyin ta'addanci da laifuffukan intanet.

Sai dai, bisa nazari, babu wani rahoto da ya nuna cewa sojojin Amurka 'sun kama' wadannan mutane takwas, ko a ce ma dai an kama su ko da a nan Najeriya ne, kawai dai an ce an rike kadarorinsu.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi kuskuren kai hari, sun kashe fararen hula kusan 200 a Borno

Bincike ya nuna babu inda sojojin Amurka suka kama 'yan Najeriya 8 kan ayyukan ta'addanci.
Sojojin Amurka da suka shiga wata gasa a sansaninsu na Buehring da ke Udairi, a Kuwait. Hoto: YASSER AL-ZAYYAT/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Gaskiyar da aka gano kan wannan ikirari

Binciken da aka gudanar, ya nuna cewa wannan ma'abocin Facebook din ya kasance yana wallafa ire-iren wadannan bayanai, kawai don neman mutane su bibiyi shafinsa, su kuma rika rarraba bidiyoyin da yake wallafawa.

Wannan karara ya nuna cewa Manny Soft yana wallafa wadannan bidiyoyi don neman mabiya, ba tare da la'akari da irin mugun dafin da hakan zai bari a cikin al'umma ba.

A karshe, bincike ya nuna cewa Amurka ta sanya takunkumi kan 'yan takwas kan zarge-zargen ta'addanci da laifuffukan intanet, amma, sojojin Amurka ba su cafke su ba.

An saki sunayen masu tallafa wa ta'addanci

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta sabunta jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da aka ayyana a matsayin wadanda ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Gwamnati ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne da nufin toshe hanyoyin samun kuɗaɗe, kadarori, da duk wani tallafi da ke taimaka wa masu tada ƙayar baya.

Jerin sunayen da ake zargin suna daukar nauyin ta'addanci sun haɗa da fitattun ƙungiyoyi irin su ISWAP, Ansaru, da IPOB, tare da mutane irin su Tukur Mamu, Fatima Ishaq da sauran su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com