Magana Ta Kare, Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Shekarau Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

Magana Ta Kare, Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Shekarau Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

  • Malam Ibrahim Shekarau ya mika takardar ficewarsa daga PDP ga shugabannin jam'iyyar a mazabarsa da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano
  • Tsohon gwamnan ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne bayan tattaunawa da neman shawarwari daga abokan siyasarsa na kwamitin shura
  • Duk da bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba a hukumance, amma bayanai sun nuna an kewaye gidansa da tambarin jam'iyyar APC mai mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance.

Shekarau ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026 a gidansa da ke Mundubawa Avenue a Kano, bayan kwanaki na tuntuba da shawarwari da ya yi da magoya bayansa, ciki har da kwamitin Shura.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ya fadi da jam'iyyar da za ta iya kayar da APC a zaben 2027

Shekarau.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar APC Hoto: Kano Online
Source: Facebook

Shekarau ya mika takardar ficewa daga PDP

The Nation ta ruwaito cewa cikin wasiƙar murabus ɗin da ya rubuta ranar 19 ga Afrilu, 2026 wadda ya aika wa shugaban PDP na unguwar Giginyu a ƙaramar hukumar Nassarawa, ya ce matakin ya fara aiki nan take.

“Ina fatan za ku karɓi wannan wasiƙa a matsayin sanarwar ficewata daga jam’iyyar PDP daga yau,” in ji shi.

An kuma aika kwafin wasiƙar ga shugaban PDP na jihar Kano da na ƙaramar hukumar Nassarawa, domin sanar da su a hukumance, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Dalilin tsohon gwamnan na barin PDP a Kano

Shekarau ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa mai zurfi da mabiyansa, domin ci gaba da harkokinsu na siyasa a wata jam’iyya daban.

Rahotanni sun nuna cewa an kawata gidansa da fastocin jam’iyyar APC, abin da ke nuni da cewa yana shirin komawa jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya soke batun komawa jam'iyyar APC, an ji dalili

Shekarau, wanda ya yi wa’adin mulki biyu a matsayin gwamnan Kano daga 2003 zuwa 2011, ana sa ran zai sanar da komawarsa APC a hukumance nan ba da jimawa ba.

Tsohon gwamnan na daga cikin waɗanda suka kafa tsohuwar jam’iyyar ANPP, wadda ya yi takara a ƙarƙashinta ya kuma zama gwamna.

Shekarau.
Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau a taron da ya kira don sanar da ficewarsa daga PDP a gidansa na Mundubawa Hoto: Ammar Sarkin Yaki
Source: Facebook

Wace jam'iyya Shekarau zai koma?

A shekarar 2014 ne Shekarau ya koma PDP bayan haɗewar jam’iyyun adawa, wadanda suka haifar da kafa APC.

Yanzu dai alamu na nuna cewa yana dab da komawa jam’iyyar APC domin ci gaba da harkokinsa na siyasa, amma dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan hakan.

Yadda APC ta yi zawarcin Shekarau

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyara gidan Malam Ibrahim Shekarau da ke cikin jihar Kano.

A wannan ziyara, Yilwatda ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin shugabannin siyasa na Arewa, inda ya bayyana yankin a matsayin cibiyar siyasar Najeriya tare da rokon Shekarau da ya dawo APC.

Da yake maida martani, Shekarau ya jinjina wa tawagar APC bisa kawo masa ziyara har gida, yana mai cewa nan da kwanaki biyu zai yanke makomarsa ta siyasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262