'An Yi Zalunci': Shekarau Ya Fadi Alakarsa da Kwankwaso bayan Tono Abin da Ya Faru Tsakaninsu

'An Yi Zalunci': Shekarau Ya Fadi Alakarsa da Kwankwaso bayan Tono Abin da Ya Faru Tsakaninsu

  • Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce yana da kyakkyawar alaka da Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje duk da bambancin siyasa
  • Shekarau ya ce kafin zaben 2019, Kwankwasiyya sun saba alkawari bayan sun kafa kwamiti, sai suka ji sunayen ‘yan takara a kafafen sadarwa
  • Tsohon gwamnan ya ce lokacin da yake neman gwamna a 2003, ba wanda ya yi tsammanin zai yi nasara, amma al’ummar Kano suka zabe shi
  • Sardauna ya ce a 2007, har Muhammadu Buhari ya ki zuwa yakin neman zabe a jihar Kano saboda ba ya son jam’iyyarsu ta ANPP ta samu nasara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya magantu kan alakarsa da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Ibrahim hekarau ya kuma tabo batun siyasar jihar Kano da kuma yadda mutanen Rabiu Kwankwaso suka ci amanarsa.

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Shekarau ya fayyace alakarsa da Kwankwaso a siyasa
Malam Ibrahim Shekarau ya fadi yadda Rabiu Kwankwaso ya ci amanarsu. Hoto: Malam Ibrahim Shekarau, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Wace alaka ce tsakanin Shekarau da Kwankwaso?

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau ya ce yana da kyakkyawar alaka da Kwankwaso har ma da Abdullahi Umar Ganduje saboda suna yawan tattaunawa.

Ya ce babu abin da zai hana su zama a inuwa daya saboda dukansu siyasa suke yi komai na iya faruwa.

A cewar Shekarau:

"Daga ni har shi (Kwankwaso) na yi imanin haka ba wai ba mu son zama inuwa daya ba ne, gaba daya a tsarin ba shi da laifi ba ni da laifi."
"Muna shirin zaben 2019 a PDP sai Kwankwaso ya sake dawowa jam'iyyar, mun zauna daga ni sai shi muka tsara abin za a yi.
"Kwankwaso ya ce mu kafa kwamiti mai mutane takwas na bayar da hudu shi ma ya kawo hudu, muna zaune ba a tuntube mu ba kawai muka ga sunayen wadanda za su yi takara a kafafen sadarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya yi gargadi kan siyasantar da tsaro bayan kalaman El-Rufa'i

"Amma daga baya na ce Rabi'u ya aka yi haka ka saba alkawari sai yake cemin mun zo a makare bayan kwamitin ya shafe watanni kan lamarin."
Shekarau ya tabo batun siyasa da alakarsa da Kwankwaso
Malam Ibrahim Shekarau ya fadi yadda Rabi'u Kwankwaso ya ci amanarsa. Hoto: Malam Ibrahim Shekarau.
Asali: Facebook

'Yadda Buhari ya yake mu a 2007' - Shekarau

Shekarau ya yi magana kan a zabe inda ya ce lokacin da yake neman gwamna a 2003 babu wanda ya yi tsammanin zai ci zabe.

Ya ce a zaben 2007, har Buhari ya yake su kuma ko Kano bai je ba domin yakin neman zaben a wancan lokaci saboda bai son su yi nasara.

Jigon APC na shirin sasanta Kwankwaso, Shekarau

Kun ji cewa wani dan jam'iyyar APC a Kano, Abdulkarim Abdulsalam Zaura ya shirya sasanta Rabi'u Kwankwaso da Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje.

Zaura ya nuna damuwa kann rashin haɗin kan da ke tsakanin manyan ƴan siyasan guda uku, ya ce siyasar da ake yi a Kano ba ta da amfani ga jihar.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya kinkimo aikin sulhunta Kwankwaso, Ganduje da Shekarau a Kano

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman doya da manja tsakanin tsofaffin gwamnonin da wasu ke ganin ya kamata su hada kansu don ci gaban jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.