Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Yaci Amanata Daga Bisani

Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Yaci Amanata Daga Bisani

  • Sanata Ibrahim Shekarau na jihar Kano ya bayyana yadda Rabiu Kwankwaso yayi masa shigo-shigo babu zurfi yayin da ya koma NNPP
  • Ya bayyana yadda Kwankwaso yace zai duba sunayen 'yan takarar bangarensa amma kwatsam ya bari har INEC ta rufe karbar 'yan takara
  • Shekarau ya sanar da cewa, sai ji suka yi Kwankwaso na fadin ba zai yuwu a dubesu ba saboda sun shigo jam'iyyar daga baya ne, lamarin da ya bata masa rai

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, yace Sanata Rabiu Musa ya ci amanarsa da mabiyansa inda yace wannan ne dalilin da yasa ya sauya jam'iyyar siyasa.

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin zantawa da shirin Siyasa a Yau na gidan Talabijin din Channels TV.

Sanata Ibrahim Shekarau
Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Yaci Amanata Daga Bisani. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sanatan mai wakiltar Kano gta tsakiya ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar NNPP zuwa ta PDP a ranar Litinin da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Akwai Ƙulalliya Tsakanin Atiku Da Ayu, Shi Yasa Ya Ƙi Murabus, In Ji Adoke

Yace shugaban tafiyar Kwankwasiyya da gangan yayi jinkirin tabbatar da yarjejeniyar da suka tsaya a kai kafin ya shiga NNPP har zuwa lokacin da INEC ta rufe karbar 'yan takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Mun mika bukatarmu ga kungiyar bayan mun koma tare da mabiyana kuma mun zauna da Rabiu Kwankwaso. Na mika bukata kuma ya amince da ita.
"Yace nan kwana daya zuwa uku zai shirya tashi bukatar daga nan mu sake zama tare da dubawa don ganin abinda zamu iya yi wa jama'armu daga mazabu daban-daban."
"Shi da ni ganin mun taba shugabantar Kano mun san manyan masu ruwa da tsaki ba tare da duban jam'iyyunsu ba.
"A tunanina ba wani babban abu bane zama ya shirya mutanensa da nawa wadanda za a iya zabe. Mun cigaba da jira. Na kai masa a ranar 10 ga watan Mayu kuma zuwa 11 ga wata na tunatar masa. Daga bisani bangarena suka yanke shawara," a cewarsa.

Kara karanta wannan

2023: Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Shekarau ya kara da cewa bai yi mamakin ganin rubutattun sunayen 'yan takara ba da INEC ta fitar daga shugabannin jam'iyyar NNPP a jihar.

Ya kara da cewa:

"A ranar 14 ga watan Mayu cikin dare, na ga sunayen da shugabannin jam'iyya suka saki, da hannu aka rubuta sunayen 'yan takarar da mazabunsu.
"A takaice, a sunayen da INEC ta fitar a ranar 18 Mayu, wasu mazabun babu sunana. Da safe na samu Kwankwaso kuma na kalubalancesa kan sunayen."
"Mun ce wannan ba zai yuwu ba saboda a dukkan sunayen sunana ne kadai babu na wani daga bangarena da ya fito.
"Zuwa 12 ga watan Augusta, INEC ta rufe dukkan kofofinta. Babu yadda za a iya mika suna daga matakin jiha ko kasa. Dole na kira taro da mabiyana domin sanar musu abinda ke faruwa cikin watanni ukun."

Shekarau ya koka bayan da yaji hirar Kwankwaso a BBC Hausa in da yake bayanin cewa:

Kara karanta wannan

Komawa PDP: Abin da Zan Fadawa Shekarau da Ina Kusa da Shi inji Shugaban NNPP

"Abun mamaki, bayan kwana biyu sai ga Rabiu Kwankwaso a BBC Hausa yana cewa babu yadda za a yi a sauraremu saboda mun shiga jam'iyyar daga baya. Jam'iyyar da muka shiga 18 ga watan Mayu lokacin da ake tantance 'yan takara da zaben fidda gwani?
“Wannan ne abun karshe da zaka kira cin amana, rashin ganin daraja da juya mutum. Manufarmu shi ne kare mutuncun juna."

Shekarau Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Bayan Wata 3 Rak a NNPP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya sanar da barin jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari zuwa ta PDP.

Wannan na zuwa ne kasa da watanni uku bayan shekarau ya bar jam'iyyar APC inda ya koma ta NNPP.

Daily Trust ta rahoto cewa, Shekarau ya bayyana barin NNPP a ranar Litini a gidansa dake Mundubawa dake jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel