Jigon APC: "Ba Aikin Tinubu ba ne Zai Sa Mu Ci Zaɓen 2027"
- Wani jigo a APC, Abubakar Yusuf ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba tare da wata matsala ba
- Abubakar Yusuf, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne ya bayyana cewa ba wai ayyukan da shugaba Bola Tinubu be zai kai su ga ci ba
- Ya ƙara da cewa APC ba ta cikin fargabar komai saboda babu ƙalubale mai ƙarfi daga ƴan adawa da ke ƙoƙarin aiki tare gabanin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, Abubakar Yusuf, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na da tabbacin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Abubakar Yusuf ya ce hasashen nasarar APC ba wai saboda gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi abin a zo a gani ba ne.

Source: Twitter
A wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels, ya bayyana cewa APC za ta kuma yin nasara ne saboda rashin ƙarfi da haɗin kai a ɓangaren jam’iyyun adawa.
APC za ta kuma nasara – Tsohon ɗan majalisa
A cewar tsohon ɗan majalisar, ya yi biris da cewa babu wata jam'iyyar adawa da ta ke da ƙarfin tunkarar APC ballantana ta ba da tsoro a kan zabe mai zuwa.
A cewar Abubakar Yusuf:
“Ina so na bayyana cewa APC za ta yi nasara a 2027. Eh, zaɓen shugaban ƙasa. Amma ba wai saboda gwamnatin Asiwaju ta yi abin a zo a gani ba ne, sai dai saboda babu wata adawa mai ƙarfi.”
Ya bayyana cewa babu haɗin kai da ƴan adawa ke buƙata wajen razana APC game da zaɓen saboda haka ko a jikinsu.
Jigon APC ya ce akwai fitattun ƴan adawa
Abubakar Yusuf ya bayyana cewa duk da cewa akwai fitattun jagorori masu ƙwarewa a cikin jam’iyyun adawa, amma rashin haɗin kai a tsakaninsu na hana su zama masu karfin fada a ji.
Ya ce:
“A ɗaiɗaikun mutane, su manyan jagorori ne masu nagarta sosai. Amma idan aka haɗa su a matsayin ƙungiya, bana ji za su iya aiki tare domin samun nasara ba.

Source: Twitter
A cewarsa, wannan rashin jituwa zai ba shugaban ƙasa Bola Tinubu damar sake samun nasara a zaɓen 2027 na tare da wata babbar matsala ba.
Ya ce:
“Saboda haka, akwai yiwuwar Tinubu zai sake lashe zaɓen 2027."
Abubakar Yusuf ya kuma jaddada cewa APC ba ta cikin fargaba ko tashin hankali dangane da zaɓen mai zuwa.
Ya ce:
“APC ba ta cikin fargaba ko kaɗan, domin ba mu da wani babban ƙalubale. Wa zai ƙalubalanci mu? Babu."
Sai dai ya ce idan har al’ummar Najeriya ne za su zama babban ƙalubale ga jam’iyyar, to akwai damar gyara kura-kuran da gwamnati ke yi kafin lokacin zaɓe.
Abubakar Yusuf ya kuma ce jam'iyyarsa ta APC na da yakinin cewa za ta ci gaba da jan ragamar mulki idan har yanayin siyasa ya ci gaba da tafiya a haka.
Gwamna ya doke koma wa APC
A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi tattauna wa da jam'iyyar APC da nufin sauya sheka zuwa cikinta, amma kamar ba za a dace ba.
Tattaunawar bangarorin biyu ba ta haifar da abin da ake zato ba, inda gwamnan ya fasa sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya duk da ƙoƙarin da dukkaninsu suka yi.
Shugaban PDP na jihar Bauchi ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta ki amincewa da bukatar da suka gabatar mata, saboda haka suka hakura da batun sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng


