"Wasunsu Hotiho ne": Tsohon Dan Majalisa Ya Gargadi Tinubu kan Dogaro da Gwamnoni a 2027
- Tsohon 'dan majalisar tarayyar Najeriya, Sanata Abubakar Yusuf ya gargadi Bola Tinubu da kada ya dogara da gwamnonin APC a zaɓen 2027
- Tsoon Sanatan Taraban ya bayyana haka ne yayin da APC ta tara gwamnonin adawa da suka sauya sheka cikinta gabanin babban zaben 2027 mai gabato wa
- Abubakar Yusuf, wanda jigo ne a APC ya yi gargadi da cewa wasu daga cikin gwamnonin ba su da ƙarfi a matakin ƙasa domin jawo kuri’u
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jigo a jam’iyyar APC, Sanata Abubakar Yusuf, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kada ya dogara da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana cewa idan har Tinubu ya sa rai da samun nasara saboda gwamnonin APC, za a iya samun matsala a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Source: Getty Images
Sanata Abubakar Yusuf ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV, inda ya ce da dama daga cikin gwamnonin ba su da farin jini na gaske a wajen talakawa.
An gargadi Tinubu game da 2027
Jaridar The sun ta wallafa cewa ana iya yin kuskure wajen kimanta ƙarfin wasu gwamnoni a fagen zaɓe, kuma lamarin ba haka ya ke ba. A cewarsa, duk da cewa gwamnoni na da tasiri a siyasance, hakan ba lallai ba ne ya fassara zuwa kuri’u a rumfunan zaɓe mai zuwa.
Ya ce akwai gibi tsakanin ikon mulkin siyasa da kuma karɓuwa a tsakanin jama’a, wanda shi ne ke yanke hukunci a ranar zaɓe.

Source: Twitter
Sanata Abubakar Yusuf ya ƙara da cewa, wasu gwamnoni na iya yin tasiri a cikin tsarin jam’iyya, amma ba su da cikakken goyon bayan talakawa.
Jagora a jam'iyya mai mulki ta APC ya kara da cewa wannan ba karamar matsala ba ce da za ta iya shafar sakamakon zaɓe idan aka jingina da su kaɗai.
An hango yiwuwar rikici a APC
Sanata Abubakar Yusuf ya bayyana damuwa kan yiwuwar rikice-rikice a cikin gida, musamman dangane da zaɓen ‘yan takara kafin zaɓen 2027.
A cewarsa, irin waɗannan sabani na iya haifar da rikici mai tsanani idan ba a sarrafa su yadda ya kamata ba, za su jawo wa jam'iyya matsala.
A cewarsa:
“Idan aka samu irin waɗannan matsaloli, za su iya janyo ruɗani da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar, wanda hakan zai iya raunana APC kafin babban zaɓe.”
Abubakar Yusuf ya jaddada muhimmancin gudanar da tsarin fitar da gwani cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai taimaka wajen kauce wa rikicin cikin gida da kuma tabbatar da nasarar jam’iyyar a 2027.
APC ba ta tsoron yan adawa - Abubakar Yusuf
A baya, kun ji cewa Wani jigo a APC, Hon. Abubakar Yusuf ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba tare da wata matsala ba duk da cewa akwai manyan 'yan siyasa da ke adawa.

Kara karanta wannan
Kalaman Atiku sun girgiza fadar shugaban kasa, ta fadi abin da Tinubu zai yi masa a 2027
Abubakar Yusuf, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne ya bayyana cewa ba wai ayyukan da shugaba Bola Tinubu ne zai kai su ga ci ba, sai dai manyan 'yan siyasar ba su da cikakken hadin kan kifar da gwamnati.
Ya ƙara da cewa APC ba ta cikin fargabar komai saboda babu ƙalubale mai ƙarfi daga ƴan adawa da ke ƙoƙarin aiki tare gabanin 2027, tare da bayyana cewa akwai yakinin Tinubu zai koma kujerarsa.
Asali: Legit.ng

