ADC Ta Gano Barazana a Dawo da Ƴan Ta'adda cikin Jama'a, Ta Gargaɗi Gwamnatin Tinubu

ADC Ta Gano Barazana a Dawo da Ƴan Ta'adda cikin Jama'a, Ta Gargaɗi Gwamnatin Tinubu

  • Jam'iyyar ADC ta yi gargadi kan sake dawo da tsofaffin ‘yan ta’adda cikin al’umma ba tare da gurfanar da su a kotu ba
  • Jam’iyyar ta ce hakan na iya ƙara ƙarfafa tashin hankali da rage ƙimar batun adalci ga waɗanda ƴan ta'adda suka gallaza wa
  • Ta buƙaci gwamnati ta bayyana cikakken tsarin tantancewa da bayan ta sake dawo da mutanen da ta kira tubabbun ƴan ta'adda cikin jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam’iyyar hamayya ta ADC ta yi gargadi cewa duk wani shiri na sake shigar da daruruwan tsofaffin ‘yan ta’adda cikin al’umma zai kawo matsala.

Ta ce za a fuskanci babbar barazana ne musamman idan aka dawo da tubabbun ƴan ta'addan ba tare da tabbatar da an yi masu shari’a ba.

Kara karanta wannan

Jigon APC: "Ba aikin Tinubu ba ne zai sa mu ci zaɓen 2027"

ADC ta soki shirin dawo da yan ta'adda cikin mutane
Shugaban kasa Bola Tinubu yayin jawabi a wata ziyara da ya kai Kano, Bolaji Abdullahi mai magana da yawun ADC Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa jam’iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu, 2026.

ADC ta yi adawa da shirin Gwamnatin Tinubu

PM News ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce dole ne a tabbatar da adalci da hukunci kafin a yi maganar sulhu ko gyara halayyar mutanen da suka kashe daruruwan jama'a.

A cewar ADC, ta’addanci ba karamin rikici ba ne, shiryayyen mataki ne na kai hare-hare da aka tsara domin cutar da ƙasa da jama’arta.

Ta ce hare-haren sun kashe rayuka da dama, sun raba mutane da gidajensu, tare da raunana tattalin arziki da tsaron ƙasar nan.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa duk wata dabara da za ta sauƙaƙa ma’anar ta’addanci ko kuma ta fifita sake gyara halayya fiye da hukunci, ba tausayi ba ne, illa rauni a tsarin yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

Jam'iyyar ADC ta nemi a bi doka

ADC ta bayyana cewa sake shigar da mutum cikin al’umma ba tare da adalci ba, ba sulhu ba ne; rashin adalci ne kawai.

ADC ta ce ba a bayyana tsarin da ake bi wajen gyara tunanin yan ta'addan ba
'Yan ta'addan da suka tuba yayin bikin yaye su a Gombe. Hoto: @AIT_Online
Source: Twitter

Ta ce:

"Hakan na aika saƙo mara kyau ga waɗanda har yanzu ke fama da radadin abin da ya faru, da kuma waɗanda ka iya tunanin shiga irin wannan hanya cewa za a iya yin sulhu bayan sun aikata laifi.”

Jam’iyyar ta kuma ce gwamnati har yanzu ba ta bayyana yadda ake tantance mutanen da ake shirin sake shigarwa cikin jama'a ba.

Ta ce haka kuma babu bayanai a kan ko an gurfanar da tubabbun ƴan ta'addan a gaban kotu, ko kuma yadda ake tabbatar da cancantarsu ta komawa cikin jama’a.

Haka kuma ta ce babu cikakken tsarin bibiyar waɗanda aka sake shigarwa cikin mutane, ko kuma shawarwari da aka yi da al’ummomin da abin ya shafa kafin aiwatar da shirin.

Tubabbun ƴan ta'adda za su dawo cikin jama'a

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris": Trump ya faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙi da Iran

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya ta kammala shirin sauya tunani da gyaran halin tsofaffin 'yan ta'adda 744 da suka fito daga jihohi daban-daban na Najeriya da wasu kasashe.

Mafi yawan tsofaffin 'ya ta'addan sun fito daga jihar Borno da ke fama da matsalar Boko Haram da wasu jihohi kamar Kano, Yobe da sauransu, wanda gwamnati ta yi aikin gyara masu tunani.

Shugaban gwamnoni Arewa, Inuwa Yahaya ya yi kira ga tsofaffin 'yan ta'addan da su yi amfani da damar da suka zamu wajen zamowa mutanen kirki a al'umma bayan gwamnati ta mayar da su ckin jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng