Abin Rabo ne: Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Ya Fito Takarar Gwamna

Abin Rabo ne: Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Ya Fito Takarar Gwamna

  • Siyasa ta dauki sabon salon da tsohon shugaban APC ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027
  • Ɗan siyasar ya bayyana cewa yana da kwarewa da hangen nesa don magance matsalolin jihar da ta ke fuskanta
  • Ya bayyana cewa gogewarsa a siyasa daga matakin kasa da kasa da na cikin gida, tare da karatun digiri na uku, sun ba shi damar shugabanci mai tasiri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ilorin, Kwara - Tsohon shugaban jam’iyyar APC ya ayyana kudirinsa na neman takarar gwamna a jihar Kwara.

Bashir Bolarinwa, ya bayyana cewa yana dakwarewa da hangen nesa na duniya da ake bukata wajen magance kalubalen tattalin arziki da shugabanci a jihar.

Tsohon shugaban APC zai yi takarar gwamna
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Bashir Bolarinwa da jiga-jiganta yayin taro a Ilorin. Hoto: Toheeb Omotayo.
Source: Facebook

Tsohon shugaban APC zai nemi takarar gwamna

Bolarinwa ya shaida cewa ya mika wasikar nuna sha’awarsa ga jam’iyya yana mai jaddada cewa ba burin kansa ya motsa shi ba sai hidima ga al'umma, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027

Ya kara da cewa doguwar gogewarsa a aikin gwamnati daga matakin kasa zuwa kasa da kasa ta ba shi kayan aikin da zai kawo ci gaba mai ma’ana.

Ya bayyana cewa karatunsa na digiri na uku a fannin hulda da kasashen duniya, da karatu daga jami’o’i daban-daban, sun kara masa fahimtar shugabanci.

Bolarinwa ya ce ya fara harkokin siyasa ne a matsayin kansila, daga bisani ya zama shugaban karamar hukuma ta Lagos Mainland sau biyu.

An fara buga gangar siyasar neman gwamna a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Wasu kujeru da tsohon shugaban APC ya rike

Daga nan Bolarinwa ya zama dan majalisar wakilai sau biyu, inda ya kara kwarewa a bangaren dokoki da tafiyar da al’amuran gwamnati a matakin kasa.

Ya kara da cewa ya nuna bajintarsa lokacin da ya jagoranci APC a Kwara a 2018, inda jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a zaben 2019, cewar TheCable.

Ya kuma ambaci rawar da ya taka a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa, inda ya inganta ka’idoji da kwarewa.

Dan takarar ya jaddada cewa burinsa hidima ne ga jama’a, yana mai cewa zai ci gaba da ginshikan nasarorin gwamnatin da ake ciki a jihar.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Ya bayyana kansa a matsayin gogaggen shugaba da ya fahimci matsalolin jama’a, yana mai cewa APC za ta ci gaba da mulki a zaben 2027.

Wannan na zuwa ne yayin da aka buga gangar siyasa ta shekarar 2027 wanda ake ganin zaben zai yi matukar zafi sosai tsakanin APC mai mulkin Najeriya da Mafi yawan jihohi da kuma ADC mai adawa duk da matsalar da ake samu a PDP.

Tsohon shugaban APC ya zama kwamishina

A wani labarin, an ji cewa majalisar dokokin Kogi ta amince da tsohon shugaban APC na jihar a matsayin kwamishina bayan bukatar Gwamna Ahmed Usman Ododo.

‘Yan majalisar sun yabawa tsohon shugaban APC bisa rawar da ya taka wajen nasarorin zabe na jam’iyya.

Sabon kwamishinan ya ce APC ba ta da hamayya mai karfi a Kogi, yana mai jaddada cewa zaben 2027 zai zama mai sauki ga jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com