Atiku: "Yadda ADC za Ta Fitar da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a 2027"
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ADC ta shirya tunkarar zaben 2027 mai zuwa a Najeriya
- Ya bayyana cewa zaben 2027 zai zama karo na ƙarshe da zai nemi shugabancin Najeriya ganin cewa shekaru sun cin masa
- Tsohon mataimakin shugaban ya ce ADC na duba amfani hanya ɗaya ko biyu wajen fitar da wanda zai fara da APC a 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a 2027 zai fito ne ta hanyar masalaha.
Ya bayyana cewa wannan ita ce hanya ta farko da suke fatan amfani da ita wajen samar da ɗan takara ba tare da an kai ruwa rana ba.

Source: Facebook
A hira da ya yi da Arise News a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu na shekarar 2026, Atiku ya ce za a ɗauki mataki na gaba idan aka gaza cimma matsaya.
Yadda ADC za ta fitar da ɗan takara
Jaridar Punch ta wallafa cewa ADC za ta mayar da hankali kan zaben fitar da gwani matukar aka gaza fahimtar juna a tsarin maslaha.
Atiku, wanda tsohon ɗan takarar shugaban kasa ne ya ce jam’iyyar na kokarin samar da hadin kai tsakanin ‘yan takara kafin daukar mataki na gaba.
A cewarsa:
“Za mu fara da kokarin cimma matsaya ta hadin kai. Idan hakan bai yiwu ba, to za mu gudanar da zaben fitar da gwani. Amma duk wanda ya fito, zan mara masa baya.”

Source: Facebook
Ya kuma nuna cewa a shirye ya ke ya janye idan wani dan takara ya samu goyon bayan ‘yan jam’iyya ta hanyar maslaha ko kuma zabe.
Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar goyon bayan Peter Obi, ya amsa da cewa babu wata matsala matukar yana cikin ‘yan takarar.
Atiku zai yi takarar karshe a 2027
Atiku ya kuma bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2027 zai zama karo na ƙarshe da zai nemi mukamin siyasa, yana mai jaddada cewa ba zai sake tsayawa takara bayan wannan zagaye ba.
Ya ce:
“Hakika, wannan zai zama na ƙarshe a gare ni, domin na dauki hakan a matsayin mataki na karshe a harkar siyasa ta.”
Lokacin da aka matsa masa ya tabbatar da hakan, sai ya ce babu wani sauyi a matsayinsa, yana mai jaddada cewa wannan shawara tasa ba za ta canza ba.
Tsohon mataimakin shugaban ya amince cewa babban kalubalen da ke gabansa yanzu shi ne yadda zai sake jawo hankalin ‘yan Najeriya su amince da shi a matsayin wanda ya dace da shugabanci.
Da yake mayar da martani kan masu ganin cewa ya wakilci tsohon zamani ne, ya ce har yanzu gogewarsa tana da muhimmanci ga ci gaban Najeriya.
Ya kara da cewa duk da cewa an ba matasa dama a shugabanci a lokuta daban-daban, sakamakon bai kai yadda ake tsammani ba.
Atiku Abubakar ya magantu kan goyon bayansa
A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Atiku ya yi magana a kan yawan masoya da ya ke da su a siyasar Arewacin Najeriya.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana da mafi girman goyon baya a Arewa fiye da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasan ya kara da cewa Arewa na kara hade kai a siyasa kuma hakan na masa amfani sosai yayin da 2027 ke kara matsowa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


