Malaman Musulunci Sun Gana da Tinubu Sun Masa Zafafan Kalamai kan Najeriya
- Farfesa Mansur Sokoto ya ce ba bishof-bishof kaɗai suka shaida wa shugaba Bola Tinubu halin da Najeriya ke ciki ba
- Malamin ya bayyana cewa Malaman Musulmi 11 sun gana da Tinubu kwanan nan kuma sun faɗa masa gaskiya kan tsaro da matsin rayuwa
- Ya ce ba daidai ba ne malaman addini su fito suna bayyana duk abin da aka tattauna da shugaban ƙasa bayan ganawa ta sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Farfesa Mansur Sokoto ya yi martani kan bayanan da bishof-bishof na cocin Katolika a Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ya yi bayan ganawarsu da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mansur Sokoto ya ce Malaman Musulmi ma sun saba ganawa da shugabannin ƙasa domin bayyana musu gaskiyar halin da al'umma ke ciki, musamman kan matsalolin tsaro da tsadar rayuwa.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Sheikh Mansur sokoto ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ganawar malamai da shugabanni
A cikin saƙon da ya fitar, Farfesa Mansur Sokoto ya bayyana cewa malaman Musulunci ma na ganawa da shugabanni suna fada masu gaskiya.
"Sun fi mu surutu ne kawai watakila kuma da manufar siyasa a wannan bayanin nasu na yanzu.
"Amma Malamai a ko da yaushe sukan nemi ganin shugaban ƙasa kuma suna koka masa halin da al'umma take ciki musamman kan lamurra guda biyu; rashin tsaro da matsin rayuwa."
Ya ƙara da cewa tun daga zamanin shugabannin Umaru Musa Yar'Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, malamai kan gana da shugabannin ƙasa suna bayyana musu halin da jama'a ke ciki.
Sai dai ya yi zargin cewa sau da yawa shugabannin na samun wasu bayanai da suka sa ba sa fahimtar ainihin matsalolin da talakawa ke fuskanta.
Ya ce:
"Kullum da wasu alƙaluma suke amfani kamar na bokaye. Talauci ya ragu da kaso kaza... tsaro ya ƙaru da kaso kaza.. kullum a tunaninsu zuwan su ya zama alheri ga Najeriya. Akan yi mai sanyi da mai zafi da su."
An yi wa Tinubu zafafan kalamai
Sheikh Mansur Sokoto ya kuma bayyana cewa bai kai makonni biyu ba da wasu Malaman Musulmi 11 suka gana da shugaba Tinubu.
Ya ce shi ma ya kamata ya kasance cikin tawagar, amma tafiyarsa zuwa Jamhuriyar Nijar ta hana shi halarta.
A cewarsa:
"Bai kai sati biyu ba yanzu Malamai 11 sun tafi wajen shugaban kasa Bola Tinubu (ni ya kamata in zama na 12 amma na tafi Jamhuriyar Nijar) kuma sun tsage masa gaskiya."
Ya ƙara da cewa da an ba shi izini, da ya wallafa doguwar takardar da aka karanta wa shugaban ƙasa tare da bayyana wasu daga cikin kalaman da aka faɗa masa.
Ya ce:
"Da sun yi izini da zan fitar da doguwar takardar da aka karanta masa. Kuma da na bayyana irin zafafan kalaman da suka faɗa masa."
Sai dai ya jaddada cewa idan malamai sun gana da shugaba a sirrance suka faɗa masa gaskiya, ba su ganin ya dace su dawo kan mimbari su bayyana duk abin da aka tattauna, sai abin da ya zama dole.

Source: Facebook
Ganawar fastoci da Tinubu
Tun da farko, Cardinal John Onaiyekan ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya nuna a fili cewa bai amince da korafe-korafen da bishof-bishof na cocin Katolika suka gabatar masa ba kan tattalin arziki, tsaro da yanayin siyasar Najeriya.
A wata hira da Arise News, Onaiyekan ya ce sun shaida wa shugaban ƙasa cewa ƙasar na fuskantar matsaloli, amma Tinubu ya mayar da martani cewa tattalin arziki na tafiya yadda ya kamata kuma ƙasar ba ta cikin halin da suka bayyana.
Ya kuma ce bishof-bishof ba su yi mamakin rashin amincewar shugaban ƙasar ba, domin manufarsu ita ce isar da abin da suka yi imanin shi ne gaskiyar halin da 'yan Najeriya ke ciki.
Hadimin Tinubu ya caccaki fasto
A wani labarin, mun ruwaito cewa Fadar shugaban ƙasa ta soki shugabannin taron Bishof-bishof na cocin Katolika kan bayyana bayanan ganawar da suka yi da shugaba Bola Tinubu.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa, Temitope Ajayi, da Daniel Bwala sun ce bishof-bishof ba su kaɗai ne masu faɗin gaskiya kan halin da ƙasar ke ciki ba, tare da cewa bai dace a fito da bayanan zaman sirri ga jama'a ba.
Sun kuma kare martanin shugaba Tinubu ga bishof-bishof, suna mai cewa ra'ayinsu kan tattalin arziki, tsaro da shugabanci ba shi ne kaɗai ra'ayin da ya dace a ɗauka ba.
Asali: Legit.ng

